Tirƙashi Mayaƙan ISWAP a wani saban hari da suka kai sun kama mutane 15 A jihar Barno.
Tirƙashi Mayaƙan ISWAP a wani saban hari da suka kai sun kama mutane 15 A jihar Barno.

Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da wasu matafiya 15 a wani sabon hari da kungiyar ta kai a Jihar borno.
Kungiyar ta sace matafiyan ne a wani shingen bincike da mayakanta sanye da kayan sojoji suka kafa a kusa da kauyen Gumsuri da ke Damboa lga a Karamar Hukumar Damboa ta jihar.
Wata majiyar tsaro ta ce Abin takaici ne yadda ƴan tayar da kayar bayan suka ci gaba da tafka ta’asarsu a yankin Dajin Sambisa Mun samu rahoto cewa ISWAP ta yi garkuwa da matafiya kusa da kauyen Gumsuri amma sun kyale mutum biyu daga cikinsu.
Suna bin duk hanyar da za su iya domin daukar sabbin mayaka sun shammaci mutane saboda yadda suka yi shigar sojoji abin da ban takaici da ban mamaci.
Majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan mayakan sun bi sawu matafiya suka yi awon gaba da su zuwa cikin Dajin Sambisa.
Yawancin mutanen da aka sace din matasa ne da suka baro garin Damboa a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Adamawa.
Daga cikin matafiyan da kungiyar ta yi garkuwa da su din har da ma’akatan kungiyoyin agaji na kasashen duniya.
Idan ba a manta ba a bayan kungiyar ta sace ma’aikatan Gwamnatin Jihar Borno shida a kan hanyar Chibok zuwa Damboa suka kuma sace motoci uku na daukar kaya a wani wurin aikin gini.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari na jihar Barno don jin tabakin ku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Yadda Rayuwar Rahama Haruna Takasance Acikin Bokiti Har Allah Ya Karɓi Rayuwarta
Tirƙashi mayaƙan ISWAP sunyi garkuwa da sojojin Nigeria biyar 5 a jihar Borno.
Kada kumanta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.