Mutuwar aure na da Sani Danja ba wai yana nufin mun kulla gaba a tsakanin mu bane kamar yadda wasu suke zato, cewar Mansurah Isah

Mutuwar aure na da Sani Danja ba wai yana nufin mun kulla gaba a tsakanin mu bane kamar yadda wasu suke zato, cewar Mansurah Isah

Mansurah Isah wanda ta kasan ce tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, wanda aka jima ana damawa da ita.

A yau jarumar ta bayyana wani al’amari game da cece-kucen da wasu jama’ar suke akan mutuwar auren su da mijin ta Sani Musa Danja.

Tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta bayyana cewa, mutuwar aure tsakaninta da tsohon mijinta Sani Musa Danja hakan baya nuna cewa sun zama abokan gaba.

Mansura Isah ta bayyana haka ga majiyar DLC Hausa ta Daily Trust a cikin wata hira da aka yi da ita a karshen mako.

Mansurah Isah ta kara da cewa: Sani shi ne uban ‘ya’yana ga shi dama abokina ne kuma abokin aiki don haka ban fahimci dalilin da yasa mutane ke ta yawan maganganu game da hakan ba.

Tsohuwar jarumar ta kara da cewa: Muna cikin duniyar zamani a yanzu kasancewar ya sake ni ba ya nufin mu zama makiya.

Sannan kuma Jama’a da dama sun yi mamaki ganin yadda suka fito a cikin wani fim mai suna ‘Fanan’ kasancewar auren su ya mutu a zahiri.

Karanta wannan labarin.

Na Gaji Da Jiran Mijin Aure Shiyasa Na Auri Kaina Na Tsawon Kwana Casa’in Cewar Wannan Budurwar

Karanta wannan labarin.

Tirƙashi Mayaƙan ISWAP a wani saban hari da suka kai sun kama mutane 15 A jihar Barno.

Karanta wannan labarin.

Tirƙashi Mayaƙan ISWAP a wani saban hari da suka kai sun kama mutane 15 A jihar Barno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button