An Kama Wani Malamin Makarantar Firamare Da Yiwa Ɗalibansa Mata Fyade
An Kama Wani Malamin Makarantar Firamare Da Yiwa Ɗalibansa Fyade

Jami’an Tsaro Sun Cafke Malaman Makarantar Firamare Kan Yiwa Dalibansu
Makafi Fyade.
Jami’an yan sanda sun kama malaman
firamare 3 kan zargin yiwa dalibansu makafi fyade.
Lamarin ya faru ne a jihar Oyo, inda malaman suke karantarwa a makarantar yara ta makafi dake jihar ta Oyo.
Kazalika, kwamishinan ilimin jihar Mr
Rahman Abdurraheem ya tabbatar da
faruwar lamarin, inda ya bayar da tabbacin cewar za a gudanar da bincike na gaskiya akan al’amarin.
A Wani Labarin Kuma Na Daban.
Wata Mata Ta Dandatse Marainan Mijinta
Saboda Zargin Yana Yin Lalata Da Matan Banza
Wata mata ta kama marainan mijinta ta
dandatsesu saboda tana zarginsa da yin
lalata da matan banza.
Lamarin ya faru ne a Aguleri dake jihar
Anambra, inda nan take minjin nata yace ga garinku nan.
Rahotanni sun bayyana cewar, shima wani
abokinsa da ya dauke shi zuwa asibiti ya rasu sakamakon hatsarin mota a hanya.
Kazalika mijin nata ya rasu ya barta da juna biyu na wata biyar.
To Allah Ya Kyauta Zamu so Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannam Lamari.
Ku Kalli Wannan Bidiyon Domin Karewa kai Daga Saran Macijai