Kotu ta umarci Gwamna Abdullahi Ganduje ya biya tarar naira Miliyan 1 akan shigar da kara karar tushe da yayi

Kotu ta umarci Gwamna Abdullahi Ganduje ya biya tarar naira Miliyan 1 akan shigar da kara karar tushe da yayi

Wata babbar kotu a Abuja karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu ta tabbatar da cewa, bangaren Sanata Ibrahim Shekarau na jam’iyar (APC) ya yi sahihin zabe na shugabannin jam’iya a matakin karamar hukuma da mazaɓu a jihar.

A ranar 30 ga watan Nuwamba ne alkalin ya amince da duk korafe-korafe da tsagin Ibrahim Shekarau ya yi ga kotun na cewa,  bangaren Abdullahi Ganduje bai yi zaben shugabannin jam’iya na mazaba ba.

Da ga bisani sai bangaren Abdullahi Ganduje ya garzaya kotu inda ya shigar da kara ya na neman kotun ta daka da sauraron karar, sannan kuma a janye matakin da ta dauka a kan zaben shugabannin jam’iya na mazaba.

Da ya ke yanke hukunci a kan ƙarar ta ɓangaren Ganduje, Mai Shari’a ya kori ƙarar ta su ya kuma caje su naira miliyan 1 sakamakon kara mara tushe da kuma bata lokacin ɗaya ɓangaren na su Shekarau.

Da ya ke yanke hukunci a kan karar ta bangaren Abdullahi Ganduje, Mai Shari’a ya kori karar tasu ya kuma caje su naira miliyan 1 sakamakon ƙara mara tushe da kuma bata lokacin ɗaya ɓangaren na su Shekarau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button