Tirƙashi Mutane Tara 9 Sun mutu a wasu garuruwan jihar Kaduna wanda ƴan bindiga suka kai saban Hari a jihar

Tirƙashi Mutane Tara 9 Sun mutu a wasu garuruwan jihar Kaduna wanda ƴan bindiga suka kai saban Hari a jihar

Mutum tara sun bakunci lahira a hare-haren da ƴan bindiga suka kai a wasu kananan hukumomi hudu na Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Samuel Aruwan ya ce hare haren sun auku ne a kananan hukumomin Chikun Zangon Kataf Igabi da kuma Zariya.

Aruwan ya sanar a ranar Juma’a cewa ƴan bindiga sun kashe mutum uku tare da jikkata wani a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da ke Karamar Hukumar Chikun a tsakanin kauyen Buruku-Udawa.

A cewarsa wanda ya samu raunin na samun kulawa a wani asibiti.
Mahara sun kuma kashe mutum daya a yankin Yola-Kadi da ke karamar hukumar inda a nan ma suka jikkata mutum daya.
Sun kuma kashe mutum biyu a kauyen Sako da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf inda aka gano gawarwaki biyu a yankin Kurfi-Magamiya.

A karamar Hukumar Zariya kuma an kashe wani magidanci a kauyen Saye.

Wanda Gwamnan jihar ya bayyana damuwarsa Nasir El-Rufai gami da addu’arsa ta samun rahama ga mamatan da kuma sauki da wadanda suka samu rauni.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci mungode.

KU KARANTA WANNAN:

Ango Wuff Yadda Akayi Bikin Sarkin Daura Mai Shekara 90 Da Budurwa Mai Shekara 20 Inda Ya Biya Sadaki 1m

 

Kalli zafafan hotunan mawakin kannywood Abdul D One tare da Amaryar sa wanda suka dauka a wajan shagalin bikin su

Jarumar Kannywood Saratu Daso ta aiki martani ga shugabannin kasar Nageriya kan ta’addancin dake kara tsamari a Arewa

Jaruman Kannywood Suna Caccakar Mulkin Buhari Akan Kisan Mutane Da ‘Yan Bindiga Sukeyi a Arewa

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button