Addu’ar muce take bin Maryam Yahaya akan wulakancin da tayiwa dan uwana, cewar Fatima
Addu'ar muce take bin Maryam Yahaya akan wulakancin da tayiwa dan uwana, cewar Fatima

Wata matashiyar budurwa mai suna Fatima wacce ta wallafa wata biidyo a shafin ta na dandalin TikTok taba bayana akan rashin kyautawar da Jaruma Maryam Yahaya ta yiwa dan uwanta.
Fatima ta fara da cewa: Yayan ta ne saurin da yayi tattaki tun daga Jihar Yobe har zuwa Jihar Kano ba tare da sanin kowa ba, domin ya sami ganin Maryam Yahaya amma sai tayi kunnen uwar shegu.
Cikin fushi ya dauki fiya-fiya yasha, har a haka jaruma Maryam Yahaya bata kalle shi ta tausaya masa ba duk da har asibiti aka kwantar da shi.
Ta kara da cewa yanzu haka kaf mutanen gidansu sun tsani jarumar kuma sun dinga yi mata addu’o’i marasa kyau, kuma alamu na nuna cewa alhakinsu ne ya kama ta.
A cikin bidiyon da ta wallafa a shafinta na TikTok, ta karasa shi tana kuka don idan mutum ya saurara zai ji shasshekar kuka yayin da ta ke kammala bidiyon.
Mu na yi wa jarumar fatan samun lafiya tare da shawartar jarumai akan gudun wulakanta masoyansu, don ba su san inda rana zata fadi ba.
Ga cikekkiyar bidiyon nan a kasa domin ku kalla.