Cin Sarauniyar Kyaun Yar Kano Ya Bar Baya Da Kura Domin An Bayyana Wani Sabon Al’amari

Cin Sarauniyar Kyaun Yar Kano Ya Bar Baya Da Kura Domin An Bayyana Wani Sabon Al'amari

A Satinan Aka Gudanar Da Gasar Sarauniyar Kyau Na Kasa Da Aka Saba Yi Duk Shekara A Victoria Island Dake Lagos Inda Zaratan Kyawawan Mata Daga Sassa Daban Daban Na Kasarnan Suka Bayyana Kwarewarsu Wajen Kwalliya Da Iya Ragwanda Suka Fito Suka Yi Juyi Aka Kuma Yi Zabe , Saide Gasar Ta Wannan Shekara Tazo Da Wani Abun Al’ajabi Da Ya Dauki Hankula Domin Kuwa A Lokuta Mabambanta Da Akayi Wannan Gasa Har Sau 44 Tarihi Ba’a Taba Samun Sanda Wata Bahaushiya Musulma Yar Arewa Mai Sa Hijabi Taci Wannan Gasa Ba Sai A Wannan Karon

Matashiyar Mai Suna Shafu Garko Taci Wannan Gasa Inda Ta Samu Lashe Zunzurutun Kudi Har Naira Miliyan Goma Da Kyautar Tsaleliyar Mota Gami Da Zaman Shekara Guda A Gida Na Alfarma Da Sauran Kyaututtuka Da Alakar Wakilcin Tallar Kamfanunnuwa Da Ta Samu

Saide A Yayin Da Wasu Daga Kudu Ke Kishi Da Kyashi ,Kuma Suna Ganin Bahaushiya Ta Lashe Gasar Mafi Akasari Kuwa A Arewa Hakan Bai Burgesu Ba Inda Ake Ta Rubuce Rubuce A Shafukan Sada Zumunta Na Gwasale Wannan Nasarar Da Shafu Ta Samu Inda Ake Ta Bayyana Hakan Da Cigaban Mai Hakan Rijiya Wasu Ma Na Ganin Da Gayya Aka Bata Kambun Lashe Gasar Dan Ayi Izgili Ga Addinin Mu Da Al’adunmu Don Basa Goyan Wannan Al’ada

Saide Kamar Yadda Aka Saba Wannan Mai Yin Wallafawar A Kafar Sadarwa Datti Asslafy Yayi Wani Tsokaci Akan Wannan Sarauniya Kamar Yadda Zakuga Cikin Bayani A Cikin Wannan Bidiyan Kasa

To Allah Ya Kyauta Amma Yan Mata Arewa Na Gani Kamar An Musu Cin Fuska Gani Ga Tsala Tsala Yan Matan Da Suka Fita Kyau A Arewa Amma Aka Bata Wannan Sarautar, Saide Kamar Yadda Kuka Sani Duk Macen Da Bata Samu Damar Halarta Wannan Gasar Ba To Bata Yarda Da Kanta Banai Shiyasa Ba’a San Tana Da Kyawun Ba Sai Ta Jira Wata Shekarar Ta Fito Ayi Gasar Da Ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button