Duk Namijin da baya kishin Matar sa yake barin ta tana wallafa bidiyo a TikTok tabbas ko kamshin Aljanna bazai ji ba, cewar Jaruma Rukayya Daway
Duk Namijin da baya kishin Matar sa yake barin ta tana wallafa bidiyo a TikTok tabbas ko kamshin Aljanna bazai ji ba, cewar Jaruma Rukayya Dawayya

Jarumar Masana’antar Kannywood Rukayya Dawayya tayi wani jan hanjali tare da gargadi akan Mazan da suke barin Matan su suna wallafa bidiyon rawa a dandalin TikTok.
Da farko Jarumar ta bada wani dan takaicaccan labarin wani abu da ya faru a akan ta wanda ta dalilin haka take gargadi akan Mazan da suke barin Matayen su kara zube, sannan kuma tayi jan hankali ga suma Matan.
Jarumar tace, akwai wasu shakikan kawayenta su ka kai mata ziyara gidanta da ke Abuja bayan ta ci kwalliya amma mijinta bai gani ba.
Sannan ta kara da cewa, Tun samun labarin sun kai mata ziyarar our ta nuna a sanar dasu cewa bata nan duk don kada su ga kwalliyarta kafin mijinta.
A cewar jarumar, har sai da mijinta ya dawo ya ga kwalliyar sannan daga bisani ta kira su ta fada musu cewa ta dawo daga inda taje.
Bayan haka Jarumar ta bayyana cewa: duk macen da ke yin kwalliya ta wallafa bidiyon kwalliyar a TikTok bata son mijinta, yayin da mazan da su ke barin matansu su na bidiyon ba sa kaunar matan kuma basa kishinsu.
Ta kara da cewa: ko kamshin Aljannah namiji mara kishi ba zai ji ba, saboda hakan fadin manzon Allah (SAW) ne.
Sannan ta kara fadin cewa, da ace mata zasu ga wasu mazan da ke kallon bidiyon su na TikTok da basu yi ba tun farko da har kuka sai sun yi.
Kamar yadda Jarumar ta fadi cewa, duk macen da take son mijinta tana killa ce kanta ne tare da boye surar jikinta, mijin ta kadai za ta bayyana wa su.
Jarumar ta kara da cewa, sannan kuma duk namijin da ya ga bidiyon matar aure a TikTok ba zai so ya kara gani ba sabida shi ma ba zai so ta shi ta yi bidiyo irin wannan ba.
Daga karshe jarumar Rukayya Dawayya ta yi addu’a inda ta ce Allah ya yi mana maganin bala’in da ya shigo wai shi TikTok.