Surutai akan juna biyun Matar shugaba Buhari bai dace ba, cewar Young Uztaz
Surutai akan juna biyun Matar shugaba Buhari bai dace ba, cewar Young Uztaz

Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sanu a ‘yan kwanakin nan ana ta zancen juna biyun mai kadin shugaba Bubari, inda mutane suke ta maganganu kala-kal a kai.
Tun bayan bayyanar wani hoton mai dakin shigaba Buhari tare da Buharin a wani kan titi, sai aka ga mai dakin nasa kamar tana da juna biyu a nan take wasu mutanen suka fara tofa albarkacin bakin su.
A yanzu kuma munci karo da wata bidiyon wanda tashar Kundin shahara ta dora a manhajar Youtube, inda Young Uztaz ta yake fadakarwa akan mutanen da suke ta maganganu akan juna biyun mai dakin shugaba Buhari.
Sannan yana nuni akan cewa, mai yasa mutane bazasu mai da hankalin su wajan abubuwan da suke addabar su a yanzu ba, sai dai suna ta maganganu akan abin da kamata ba.
Domin kuji cikekken bayani daga bakin Young Uztaz sai ku kalli bidiyon dake kasa.
Ga bidiyon nan domin ku kalla.