Advertisement

Allahu Akbar Jerin Fitattatun Jaruman Kannywood 4 Da Suka Rasu A Shekarar 2021

Allahu Akbar Jerin Fitattatun Jaruman Kannywood 4 Da Suka Rasu A Shekarar 2021

A Shekarar 2021 Masana’antar Kannywood Ta Shiga Cikin Jimami Sosai Sakamakon Rashin Wasu Fitattun Jarumanta Akalla Guda Huda ,Yayinda Muke Bankwana Da 2021 Mun Tattaro Muku Jerin Wadannan Jarumai Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Da Kuma Fatan Allah Ya Jikansu Da Rahma

1- Sani Garba Sk

Sani Garba Sk Ya Rasu Ranar Laraba 15 Ga Watan Disamba 2021 Allah Yayiwa Fitattacen Dan Wasan Kwakwayon Fina Finan Hausa Na Masana’antar Kannywood Sani Garba Wanda Aka Fi Sani Da Sani Sk Rasuwa , Kamar Yadda Bbc Hausa Suka Rawaito Cewa Jarumin Ya Rasu Ne A Birnin Kano , Bayan Doguwar Jinyar Da Yayi , Rahoton Yace Fitaccen Forudusa Abdul M Amart Mai Kwashewa Ne Ya Tabbatar Da Rasuwar Dan Wasan

2- Ahmed Tage

Allah Yayiwa Fitattacen Jarumi Kuma Mai Daukar Hoto A Masana’antar Shirya Fina Finan Hausa Ta Kannywood Alhaji Aliyu Ahmed Tage Rasuwa , Kamar Yadda Muka Sami Labarin Ya Rasune A Ranar Litini 13 Ga Watan Satumba A Jihar Kano Bayan Yayi Fama Da Yar Gajerar Rashin Lafiya

3- Zainab Both

Tsohuwar Jarumar Masana’anatar Shirya Fina Finan Hausa Ta Kannywood Hajiya Zainab Both Musa Ta Rasuwa Ne A Daren Ranar Alhamis 1 Ga Watan Yuli A Jihar Kano , Marigayiyar Itace Mahaifiyar Shahararrun Yan Wasan Kannywood Uku Da Suka Hada Maryam Both, Ramadan Both , Amude Both , Inda Akayi Jana’izzar Ta A Safiyar Juma’a 2 Ga Watan Yuli , Da Misalin Karfe 8:00 A Gidanta Dake Kallon Premium Hospital Court Road

5-Isyaku Forest

Isyaku Forest Fitattacen Mawakine A Masana’anatar Kannywood, Marigayin Yayi Fice A Wakokin Jam’iyyar Apc, Ya Rasu Ne A Ranar 4 Ga Watan Satumba Bayan Yayi Fama Da Rashin Lafiya Na Tsawan Lokaci

Kalli Bidiyan Cikakken Bayani Game Da Marigayan

To Allah Ya Jikansu Da Rahma Ya Kyauta Makomar Magabanta Mu In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Jika Da Imani.

Ku Kara Karanta Wannan Labarin

Bayyanar Bidiyon Wata Soja Tana Sumbatar Wani Ɗalibin Jami’a Ya Tayarda Ƙura A Kafafen Sada Zumunta

Wannan Rashin Kunyace ‘Yar Musumai Ta Zamto Sarauniyar Kyau Cewar Hukuma Hisbah Ta Jihar Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button