Tirƙashi ƴanbindiga sun ƙone wani mutum kurmus acikin motarsa har lahira.

Tirƙashi ƴanbindiga sun ƙone wani mutum kurmus acikin motarsa har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga a ranar Laraba data gabata sun kone wani mutum kurmus a cikin motarsa a Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.

Wanda lamarin ya aukune ajiya laraba Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina wanda ke wakilcin mazabar Faskari shi ne ya tabbatar da lamarin da cewa ƴan bindigar sun banka wa mutumin wuta da ransa wanda har saida ya ce gagari kunan.

Dan Majalisar ya ce akwai mutanen da ƴan bindigar suka kashe yayin da suka yi awo gaba da wasu da dama.

Da yake zantawa da wakilinmu yace wannan hari daya ne daga cikin hare-hare hudu da suka auku cikin makon nan.

Sun kai hari kauyen Kwakware inda suka yi awon gaba da mutum 17 kuma galibinsu mata ne.

Bayan kwana daya da faruwar hakan ne kuma ƴan bindiga suka tare wani direba wanda suka kone shi kurmus a cikin motarsa.

Ko a shekaran jiya Talata sai da suka kashe wasu mutum bakwai sannan suka yi awon gaba da mutum biyar.

Abin takaicin shi ne yadda duk wuraren da wadannan hare-hare ba su da wata tazara mai nisa tsakaninsu da wani shingen binciken ababen hawa da dakarun soji suka kafa a cewarsa.

A kan haka ne mazauna suka tare babbar hanyar Funtua zuwa Sheme domin nuna fushinsu kan hare-haren ƴan bindiga da suka tsananta a yankunansu.

Duk wannan dai na zuwa ne bayan makonni biyu da aka yi ta tayar da jijiyoyin wuya biyo bayan kone wasu fasinjoji 38 da ’yan bindiga suka yi a Jihar Sakkwato.

A makon da muka yi bankwana da shi ne Gwamna Bello Masari na Jihar Katsna ya jagoranci tawagar wasu dattawa da suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari kokensu kan kashe-kashen mutane da ake yi a jihar.

Ko da suka kai wa Shugaba Buhari ziyarar ya ba su tabbacin cewa ana yin duk wata mai yiwuwa domin magance matsalar tsaro yankin Arewa maso Yamma da kuma sauran sassan kasar.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.

KU KARANTA WANNAN:

Tirkashi Ana Zargin Jarumar Film Din izzar so Da Karuwanchi Aisha Najamu

Waɗannan Abubuwan Sune Suke Lalata Rayuwar Auren Hausawa Musamman A Arewachin Nigeria

Wannan Rashin Kunyace ‘Yar Musumai Ta Zamto Sarauniyar Kyau Cewar Hukuma Hisbah Ta Jihar Kano

Masha Allah: An bayyana jaruman Kannywood wanda suka yi bautar kasa sannan kuma da garuruwan da aka tura su

 

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button