Tirƙashi Mahara sun kai farmaki masallaci tare da sace mutum hudu a jihar Taraba.
Tirƙashi Mahara sun kai farmaki masallaci tare da sace mutum hudu a jihar Taraba.

Mahara sun kai farmaki masallaci tare da sace mutum hudu a garin Tella da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba a daren ranar Laraba.
Wani mazaunin garin Tella Suleiman Rabiu ya shaida wa ɗaya daga cikin manema labaranmu na Dalatopnews cewa wasu ƴan bindiga kimanin 12 ne suka zagaye masallacin a lokacin Sallar Isha’i sannan suka yi garkuwa da mutum hudu.
Majiyar ta bayyana cewa bayan katse mutane yayin da suke sallah maharan sun yi awon gaba da wasu mutane a masallacin.
Mutumin ya ce jim kadan bayan tafiyarsu, ’yan bindigar suka saki mutum daya daga cikin mutum hudu da suma sace.
Mazauna yankin Gassol na fuskantar hare-haren ƴan bindiga da ke zargin wadanda suka yi kaura ne daga Jihar Zamfara bayan fatattaka da suka sha a hannun dakarun sojin kasar nan a baya-bayan nan.
Rahotanni sun bayyana cewa cikin sati uku an yi garkuwa da sama da mutum 25 wadanda yawancinsu manoma da ƴan kasuwa ne daga yankin.
Mutane da maharan suka yi garkuwa da su yayin sallar Isha’i a a masallacin sun hada da Alhaji Yahaya Aminu Dali da Alhaji Hussaini, wanda shi ne shugaban masu sayar da kayan hatsi na yankin.
Kakakin ƴan sandan jihar DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar harin.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci.
KU KARANTA WANNAN:
Hatsarin Motar Da Lawan Ahmad Yayi Har Ya Mutu Yanzu Aka Bayyana Gaskiyar Lamari innalillahi
Maryam Yahaya Batajin Shawara Shiyasa Abubuwa Suke Faruwa Ga Rayuwarta Cewar Datty Assalafy
Ali Isa Jita ya faranta zuciyar matarsa Nafisa da wasu zafafan kalaman soyayya
Kada Kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.