Da kyar na shawo kan mahaifina kafin ya amince na shiga gasar kyau, cewar Shatu Garko

Da kyar na shawo kan mahaifina kafin ya amince na shiga gasar kyau, cewar Shatu Garko

Shatu Garko Sarauniyar kyau ta 44 a Najeriya ta shaida yadda ta samu nasarar shawo kan mahaifinta har ya amince ta shiga gasar.

Budurwar mai shekaru 18 ta zama mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar tun da aka fara a shekarar 1957 kamar yadda ta shaida wa The Punch a wata hira da jaridar ta yi da ita.

Mahaifiyata dama tana goyon bayana kuma ta na nuna min ba wani abu mai wahala bane, amma mahaifina ne baya so.

Ya damu don gudun kada su tilasta ni in cire hijabi na ko insa kayan wanka ko kuma su mayar da ni gefe saboda rufe surar jikina da nayi. Mahaifiyata da ni mun taru muna ba shi baki sannan ya amince, da amincewarsa na yi gasar.

A cewarta, mutane sun dinga caccakar ta wasu su na cewa ta koma makaranta ta yi karatu maimakon shiga gasar.

Eh ba ‘yan arewa kadai ba, har wasu daban sun caccake ni. Wasu sun dinga cewa zan bata sunan gasar. Akwai wadanda su ka dinga cewa zan kai ‘yan Boko Haram ko kuma makiyayan Fulani cikin gasar. Kawai share su nayi.

Garko ta lashe gasar ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Disamba inda ta kasance mace ta farko daga Kano da ta bige mutane 17 ta ci nasarar. An yi gasar ne a jihar Legas kuma ta samu kyautuka kamar N10m, zama a katafaren gida na shekara daya, sabuwar mota da kuma damar tallata kaya da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button