Advertisement

Innalilahi wainna ilaihir raji’un Jami’an tsaro a Jihar Ondo sun cafke wani mutum dauke da kan mutum a cikin buhu.

Innalilahi wainna ilaihir raji'un Jami’an tsaro a Jihar Ondo sun cafke wani mutum dauke da kan mutum a cikin buhu.

Jami’an tsaro a Jihar Ondo sun cafke wani mutum dauke da kan mutum a cikin buhu.
A safiyar yaune muka sami saban rahoto daga jihar ondo wanda rahotan ya nuna mana cewa ankamashine da kan mutum a cikin buhu.
Mutumin ya shiga hannun ƴan sanda ne a ranar Alhamis a yankin Ajagbale da ke Ondo, dauke da kan mutum a cikin buhu.
A cewar ƴan sandan bayan gudanar da bincike mutumin ya amsa cewa ya samo kan mutumin ne saboda yana so ya yi tsafi da shi domin ya yi arziki.
Kwamishinan ƴan Sandan jihar Oyeyemi Oyediran ya ce sun yi nasarar sake cafke wani mutum bayan samun wasu bayanan sirri cewa mutumin ya dauki budurwarsa zuwa otal wanda a nan ne ya kashe ta tare da datse mata kai.
An cafke wanda ake zargin ne a yayin da yake kokarin tserewa daga otal din a ranar 17 ga watan Disamba 2021.
Bayan cafke shi an shiga dakin da ya datse kan matashiyar inda aka same ta cikin jini a kwance.
Kwamishinan ya ce tuni aka fara  gudanar da bincike kafin mika su zuwa kotu.
To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Kada ku manta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button