Tofa ƴan bindiga sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna suka kuma kashe wasu matafiyan a jiya.

Tofa ƴan bindiga sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna suka kuma kashe wasu matafiyan a jiya.

A karo na biyu cikin sa’a 24 ƴan bindiga sun sake tare babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna sannan suka karkashe matafiya a jiya.

Akalla matafiya shida ne aka sace yayin harin sannan aka yi awon gaba da wasu da dama.

Lamarin dai ya faru ne Unguwar Geda da ke kusa da Zankoro wajen misalin karfe 3:00 na yammacin Alhamis.

Wajen dai ya yi kaurin suna wajen satar mutane.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce har da kaninsa a cikin wadanda aka sace sannan bani da abin cewa saidai Allah ya kuɓutar da su Ameen.

Maganar da muke da kai yanzu ina tabbatar maka da cewa mutum shida sun mutu kuma ba mu san nawa aka sace ba. Kanina na cikin wadanda aka sace din.

A  zahirin gaskiya ma da yamman nan har masu garkuwar sun tuntubemu inji shi.

Kazalika shi ma wani mazaunin yankin Udawa Mohammed Umaru ya ce an kashe kaninsa yayin harin.

Muna cikin tashin hankali matuka sun kashe kanina.
Ba mu dade da dauko gawarsa ba don yi masa jana’iza inji shi.

Manema labaranmu sun kuma gano cewa ƴan bindigar sun kuma fasa wata tawagar motocin da jami’an tsaro da ƴan sa kai suka yi wa rakiya yayin harin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wani jawabi a hukumance daga Gwamnatin Jihar ko daga Rundunar ƴansandan saboda Kakakin Rundunar ASP Mohammed Jalige bai amsa kiran wayar wakilinmu ba.

‎A baya dai ƴan sandan sun ce sun sami nasarar kubutar da matafiya 40 da aka sace a kan hanyar ranar Laraba.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci.

A harkulum nine naku A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews ɗauke da labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Tirƙashi Mahara sun kai farmaki masallaci tare da sace mutum hudu a jihar Taraba.

Hatsarin Motar Da Lawan Ahmad Yayi Har Ya Mutu Yanzu Aka Bayyana Gaskiyar Lamari innalillahi

Maryam Yahaya Batajin Shawara Shiyasa Abubuwa Suke Faruwa Ga Rayuwarta Cewar Datty Assalafy

Tirƙashi ƴanbindiga sun ƙone wani mutum kurmus acikin motarsa har lahira.

Kada ku manta ku danna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button