‘Yan Boko Haram sun harba rokoki a Maiduguri a lokacin da Buhari zai kai ziyara a yau

'Yan Boko Haram sun harba rokoki a Maiduguri a lokacin da Buhari zai kai ziyara a yau

A lokacin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara Maiduguri a yau, Boko Haram sun harba roka a filin jirgin sama na Ngomari a yau.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa roka ɗaya ya sauka ne a yankin Ajilari kusa da filin jirgin sama inda sansanin sojoji ya ke.

Wata majiya ta ce mutum ɗaya ya rasu a Ngomari, inda wasu kuma su ka samu raunuka a Ajilari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button