Tirƙashi jami’an ƴansandan jihar Legos sun Sami Nasarar cafke wasu mutum biyu da suka sato mota ƙirar Toyota.

Tirƙashi jami'an ƴansandan jihar Legos sun Sami Nasarar cafke wasu mutum biyu da suka sato mota ƙirar Toyota.

 Satar mota yazama ruwan dare a Nigeria mu sannan yankunan Legos Cikin Nigeria.

Jami’an tsaro sun yi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi ƴan fashi da makami ne wadanda suka hada da Kenneth Akpa da Adebayo Michael bisa zargin satar mota a Jihar Legas.

Rundunar ƴan sandan Gundumar Iperu ta kame wadanda ake zargin ne bayan samun labarin cewa wata mota da ake zargin sato ta aka yi kirar Toyota Corolla 2008 an gansu ne a wani garejin kanikawa da ke kan titin Ogere iperu inda ƴan fashin ke kokarin gyara ta.

Kakakin rundunar ƴan sandan Abimbola Oyeyemi ya shaida wa manema labarai a makon da ya gabata cewa Shugaban ofishin ’yan sandan yankin Iperu DPO ya tura jami’ansa zuwa wurin da aka kama wadanda ake zargin biyu tare da kwato motar mai lamba MUS 599 GB.

A cewarsa, an tuntubi mai motar, mai suna James John Ushahemba, mazaunin garin Ahoyaya da ke Legas, kuma ya isa Iperu.
Ushahemba ya bayyana cewa Wasu mutum biyu dauke da makamai ne suka kai masa hari a gidansa a ranar 20 ga Disamba 2021 da misalin karfe 1:30 na tsakar dare.
 Ya kuma kara da cewa ƴan fashin sun yi masa fashin motarsa kirar Toyota Corolla, tare da wayoyin sadarwarsa uku da tsabar kudi Naira dubu 30 ta hanyar yi masa barazana da bindiga.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin Ku akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci.

KU KARANTA WANNAN:

innalillahi ‘Yam Matan TikTok Zasu Kashe Wata Da Duka Acikin Gidansu – Suddeenly

Rundunar sojojin Nigeriya sun sami nasarar kashe jami’an ISWAP mutane ashirin da biyu 22 a Nigeria.

 

Da kyar na shawo kan mahaifina kafin ya amince na shiga gasar kyau, cewar Shatu Garko

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button