Dakarun runduna sojojin Najeriya a Jihar Inugu sun kama wani jagoran haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB)

Dakarun runduna sojojin Najeriya a Jihar Inugu sun kama wani jagoran haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB).

 

Haryanzu ƴan ƙungiyar (IPOB) basu hakura a suna kayan batun su dakuma ƙudirinsu.

Dakarun runduna ta 82 ta sojojin Najeriya a Jihar Inugu sun kama Godwin Nnamdi wani jagoran haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta yan aware a kudancin ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarun rundunar Operation Golden Dawn ne suka kama wanda ake zargin a ranar Kirsimeti.

Janar Nwachukwu ya ce an kama gawurtaccen shugaban ƙungiyar yayin wani sintiri a Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.

Sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 da harsasai da kuma wayar salula daga hannun Godwin Nnamdi a cewar janar ɗin.

An kama jagoran IPOB/ESN yayin wani samame a wani sansani da ake zargin shi ne matsugunin ƙungiyar a Dajin Akpowfu da ke Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas inji shi.

To jama’a zamuso mukarɓi ra ayoyin a kan aukuwar lamarin don jin tabakinku zamuso kubiyomu ta sahinmu na tsokaci.

A harkulum Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews Dauke da labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Wallahi Aure Nakeso Na Gaji Da Kwana Ni Kaɗai Acikin Sanyin nan Cewar Wata Budurwa

Shugaban Sojan Ƙasa Ya Umarci Sojar Data Auri Ɗan Bautar Ƙasa Daya Saketa Bayan Aure

 

Lukman Labarina da Umar tare da Adama Dadin kowa sun lashe kyautar gwarzon shekara ta 2021

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button