Tofa abinda ake jira yafaru yafaru yadda su P-Square suka gudanar da bikin shirya warsu.
Tofa abinda ake jira yafaru yafaru yadda su P-Square suka gudanar da bikin shirya warsu.

A ranar bikin Kirsimeti ce fitattun ƴan biyun mawakan nan Peter da Paul da aka fi sani da P-Square suka shirya.
Ƴan biyun dai sun hade ne bayan sun shekara biyar a rabe suna gudanar da harkokinsu.
A watan Nuwamba ne suka sanar da sulhun a wani faifan bidiyo da suka fitar sun rungume juna a wani daki yayinda wasu a gefe suka rika tafawa.
Haka nan kuma manajansu wanda shi ne babban yayansu Jude Okoye shi ma yana cikin dakin.
An dade ana ta kokarin sulhunta mawakan ƴan uwan juna tun rabuwarsu a shekarar 2016 amma abin ya ci tura.
Daga cikin abubuwan da suka kawo musu matsala akwai matsayin yayansu Jude da kuma auren Paul da budurwarsa Anita.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin sulhun akwai Tony Elumelu Kate Henshaw Linda Ikeji Jude Okoye Lola Omotayo da sauransu.
Wani karin aramashi na bikin shi ne yadda ƴan biyun suka shirya tsakanin wasu abokan guda biyu wato Timaya da J. Martins da su ma suka yi shekara kusan bakwai suna rikici.
Mawakan sun yi waka tare a bikin a wani irin abu da masoyansu suka dade suna sha’awar sake gani.
A taron sun rera wakokinsu na Chop my money da Ifunaya da sauransu.
A tsakiyar bikin ne Mr P. ya tsayar da komai ya ce suna neman afuwar masoyansu bisa kuskuren da suka yi na rabewa sannan ya umarci kaninsa suka tsuguna tare suna ba masu kallon haƙuri sannan a karshe aka sa wakar ‘Alingo inda a ciki ake cewa ‘P-Square is back again sannan babban abokinsu May D ya fito inda suka yi wakar nan da suka yi a
tare ta ‘Chop my money.
Daga cikin fitattun wakokin ƴan biyun akwai ‘Chop my money’ da ‘Ifunaya’ da ‘Alingo’ da ‘Personally’ wanda ake irin rawar Michael Jackson da Do me’ da ‘Testimony’ da ‘Bizy body’ da sauransu.
Bikin sulhun wanda suka sa wa suna P-Square reunion concert’ ya samu halartar manyan baki daga cikin mawaka da yan siyasa da ƴan kasuwa na kasar nan.
To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin Ku akan wannan lamari wanda ba a yi tunani a kwana kusa Don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Bayani Kan Jerin Jaruma 12 Da Tauraruwar So Tafi Haskaka A Shekarar 2021
Tirƙashi ƴan daba sun Tarwatsa masu Taron PDP wanda lamarin yatada kura a kafar sada zumunta.
Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.