Daga Yanzu Bazan Sake Yin Garkuwa Da Mutane Ba Yanzu Na Saki Wayanda Suke Hanunmu Cewa Turji
Daga Yanzu Bazan Sake Yin Garkuwa Da Mutane Ba Yanzu Na Saki Wayanda Suke Hanunmu Cewa Turji

Rahotannin Daga Jihar Zamfara A Nijeriya Na Cewa Kasurgumin Dan Fanshi Dajin Nan Da Aka Fi Sani Da Suna Bello Turji Ya Saki Wasu Gomman Mutane Da Suka Dade Suna Tsare A Hannunsa
Rikakken Dan Fashin, Na Cikin Manyan Jagororin Yan Fashin Dajin Da Suka Fi Kaurin Suna Wajen Kashe -Kashe Da Satar Mutane Don Neman Kudin Fansa Musamman A Tsakanin Jihohin Zamfara Da Sokoto
Jaridar Daily Trust Ta Ambato Wasu Majiyoyi Da Ke Cewa A Watan Jiya, Bello Turji Ya Rubutawa Masarautar Shinkafi Wasika Inda Yake Jadadda Aniyyarsa Ta Hawa Teburin Tattaunawa Da Nufin Ajiye Makamansa Da Kuma Rungumar Zaman Lafiya
A Cewarta Sakin Gomman Mutanen Wani Bangare Ne Na Tattaunawar Da Ake Yi Da Turji
Bakin Gulbi Bello Turji Ya Ajiye Su A Kusa Da Kauyen Mabera
Da Misalin Karfe Biyar Na Maraice Zuwa Shida Shi Turji Ya Sako Wadannan Mutane Kuma Aka Je Aka Zo Dasu Zuwa Area Command Na Rundunar Yan Sanda Da Ke Nan Cikin Garin Shinkafi
Yace Ba Da Jimawa Ba Kuma Aka Wuce Da Su Zuwa Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara
Ya Kara Da Cewa Wasu Cikin Yan Uwan Wadanda Aka Sakon Sun Gana Da Su Har Ana Murna
Da Aka Tambayi Wannan Shaidan Ko Me Kwaso Wadanda Aka Sakin Sai Ya Ce An Kawo Su Ne A Motoci , Bakin Gulbi Tutji Ya Ajiye Su A Kusa Da Kauyen mabera Da Yake Kusa Da Shinkafi
Inda Aka Bayyana Cewa Turji Ya Saki Dukka Wayanda Yayi Garkuwa Da Su Saboda San Ayi Sasantu Kamar Yadda Zakuga Bidiyan A Kasa
Masu Sauraranmi A Koda Yaushe Bayan Kun Kalli Wannan Bidiyan Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci Sannan Muna Da Bukatar Inda Wannan Ne Karan Ka Na Farko Da Ka Dannan Mana Alamar Kararrawar Sanarwa Domin Samun Shirya Shiryanmu A Koda Yaushe.