Ina neman afuwar ‘yan kasa akan wakar da nayiwa shugaba Buhari kuma zanyi wakokin da zasu warware kalaman da nayi masa, inji Ibrahim Yala hayin Banki

Ina neman afuwar 'yan kasa akan wakar da nayiwa shugaba Buhari kuma zanyi wakokin da zasu warware kalaman da nayi masa, inji Ibrahim Yala hayin Banki

Mawaki Ibrahim Yala Hayin Banki wanda ya yiwa shugaba Buhari wakar yau nageriya riko sai mai gaskiya baba Buhari kai muke so nageriya,

Ya nemi afuwar ‘yan kasa da su yafe masa akan wannan wakar da yayi sannan kuma ya bayyana cewa, zai yi wasu wakoki wanda zasu warware kalaman da ya yiwa shugaba Buhari.

Salamu Alaikum Warahmatullah. Ina Mai sanar da masu bibiya ta a kafar sadarwa ta zamani cewa. Ni Ibrahim Yala Hayin Banki (Mai Bakandamiyar wakar Buhari wacce na Sanya ta a wannan post din danayi. Zan saki sababbin wakoki na guda biyu idan Allah Ya kaimu 1-1-2022 Insha Allah. Wakokin sune: Yan Nigeria ku
yafemin da Kuma Taron tsintsiya Babu shara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button