Gwamnatin Kasar Nageriya ta gano masu daukar nauyin ‘yan Boko Haram da kuma ISWAP
Gwamnatin Kasar Nageriya ta gano masu daukar nauyin 'yan Boko Haram da kuma ISWAP

Kamar yadda kuka sani har kullum asirin wadanda basa son cigaban kasar nan tonuwa yake, wanda a yanzu muka sake samin wani labarin akan wasu mutane da suke daukar nauyin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.
Kamar yadda Gwamnatin Nijeriya ta fadi cewa, ta bankado masu daukar nauyin ta’addanci a ƙasar har guda 96, musamman ma wadanda suke goyon bayan Boko Haram da ISWAP.
Kamar yadda Ministan yada Labarai na kasa “Lai Mohammed” ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a kan irin nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu na yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Bayan haka ya kara da cewa, anata bangaren a nazarin da Hukumar hada hadar Kudi ta Sirri ta kasa wato “NFIU”, a shekarar 2020-2021 ta bankado masu daukar nauyin ta’addanci a Nijeriya.
Abokan harkar masu daukar nauyin ta’addanci su 424 wanda da sa hannun wajen kamfanunuwa 123 da kuma kamfanonin canjin kudi 33, gami da bayyana ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane 26 da kuma masu taimaka musu guda 7.
Nazarin ya haifar da kama mutane 45 da kwanan nan za’a yanke musu hukuncin a kotu da kuma kwace kadarorin su.
Game da daukar nauyin ta’addanci “NFIU” na musayar bayanan sirri da kasashe 19 a kan Boko Haram, ISWAP, fashin daji da garkuwa da mutane.
Da ga lokacin 2020-2021 NFIU ta maida kudaden damfara da su ka kai dala 103,722,102.83, 3,000, fam 7,695 da kuma dalar singapore 1,091 ga kasashe 11.