Ƴan bindiga sun kai hari garin Nasarawar Mai fara a jihar Zamfara bayan da suka sara wa jama’ar kauyukan wajen tarar zaman lafiya ta naira miliyan 40.

Ƴan bindiga sun kai hari garin Nasarawar Mai fara a jihar Zamfara bayan da suka sara wa jama'ar kauyukan wajen tarar zaman lafiya ta naira miliyan 40.

Ƴan bindiga sun kai hari garin Nasarawar Mai fara a jihar Zamfara bayan da suka sara wa jama’ar kauyukan wajen tarar zaman lafiya ta naira miliyan 40.

Wani mutumin Nasarawar Mai-fara ya shaida wa mane ma labaranmu cewa a daren ranar Jumma’a ne aka yi jana’izar mutanen da ‘yan bindigar suka halaka a harin bazatar da suka kai.

Mutumin ya ce kafin wannan iftila’in ya same su sai da ƴan bindigar suka zo suka ce su hada kudi su mazauna yankunan domin siyan zaman lafiya haka kuma aka yi suka tara naira miliyan 40 suka basu.

To amma sai gashi ba zato ba tsammani suka shigo musu garuruwa suka fatattake su bayan kashe musu mutane fiye da 20 in ji mutumin.

Ya ce Abin takaicin ma shi ne bayan sun kashe mana mutane sai da aka kwana biyu sannan suka bar mu muka je muka dauko gawawwakin aka yi musu sitira

Mutumin ya ce Da mukaga abin ba sauki muka kira jami’an tsaro su zo ba suzo ba har sai da ƴan bindigar suka shafe sa’a biyu da rabi ana harbe- harbe da su.

A wannan hari an kashe mutum 11 tare da raunata wasu mutum hudu sannan an yi awon gaba da mata da dama in ji mutumin.

Su kuwa jama’ar garin Tofar Magami a yankin karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfarar gudun hijra suka yi in da ƴan bindigar suka kankame garin.

Wani ɗan asalin garin da suka yi gudun hijra ya shaida wa Dalatopnews cewa a halin da ake ciki yanzu a garin nasu ba bu mutum ko guda barayin dajin ne suka kankame tare da kafa sansaninsu a yankin.

Mutumin ya ce A yanzu haka barayin na zaune a cikin gidajen mutanen da suka tsere kuma irin wulakancin da suke mana a yanzu bayan kashe mana mutane su duake su har ta kai yanzu ma a gabanka za a yi lalata da matarka kana gani.

KU KARANTA WANNAN:

Bayan Sacewa Hanifa Da Kasheta, Yanzu Aka Kama Wata Mata Mai Satar Ƙananan Yara A jihar kano

Zazzafan Martanin Zagin Maryam Yahaya Ga Masu Sa Mata Ido Tun Lokacin Da Ta Samu Sauki

Tirƙashi Ashe Wannan Ne Hukunchin Da Aka Yanke A Shari’ar Malam Abduljabbar A Jiya

Tirƙashi wasu mahar ƴan bindiga sun kai hari akan babura garin Daddara dake jihar Zamfara inda suka kashe mutane da dama ciki har da magajin garin da dogarai uku.

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button