Cikakken Bidiyan Shagalin Bikin Mai Shadda Da Hassana Muhammad

Cikakken Bidiyan Shagalin Bikin Mai Shadda Da Hassana Muhammad

Masha Allah Kamar yadda kuka sani a satinan ne masana’anatar kannywood ta turnuke da shagalin bikin furodusa abubakar bashir mai shadda da tsaleliyar amaryarsa hassana muhammad

Saide a shagulgulan bikin har da wasan kwallo da wasan cin kaza aka gudanar wadda anyi shi ne kafin biki inda kuma a yau muka samu cikakken bidiyan yadda aka gudanar da shagalin bikin bayan an daura auren kamar yadda zakuga bidiyan anan kasa

A cikin bidiyan zakuga yadda manya jaruman kannywood mata da maza ke kwashe rawa wadda suka hada da ado gwanja, momy gombe, adam a zango da dai sauransu

Masu sauraranmu bayan kun kalli wannan bidiyan bikin zamu so karben ra’ayoyimku a sahen mu na tsokaci sanna da ka danna mana alamar kararrawar sanarwa.

KAMAR yadda ake aure, haka ma ake saki. Wasu lokutan shi saki zuwa kawai ya ke yi ba tare mace ta yi tsammanin sa ba saboda rashin tasirin abin da ya haddasa saki.

Ga wasu shawarwari da duk wata sabuwar bazawara za ta yi amfani da su domin inganta rayuwar ta:

1: Ki mai da lamarin ga Allah: 

Ki sani, mutuwar auren ki ba ita ce tashin alkiyamar ki ba. Sau tari wani sakin shi ne zai zame maki alheri. Don haka ki tattara lamuranki ki damƙa wa Allah. Kada ki zargi kowa a kan mutuwar auren ki ko da kuwa ya bayyana wani na da hannu a ciki.

2: Ki Riƙa Shiga Mutane: 

Ki guji kaɗaita kan ki saboda auren ki ya mutu. Shiga cikin mutane ki yi rayuwar ki kamar yadda duk wata ‘ya mace ta ke yi. Yawan kaɗaita kai zai iya jawo maki faɗawa wasu tunanin da za su iya yi wa lafiyar ki da rayuwar ki illa.

3: Ki Kula Da Jikin Ki: 

Kada ki ce tunda auren ki ya mutu za ki daina kula da jikin ki. Yi kwalliyar ki, ki gyara jikin ki. Kashe ɗauri musamman idan za ki fita unguwa.

4: Samu Abin Yi:

Idan da man ki na da sha’awar karatu kuma ki na da damar yi, shiga makaranta.

Idan kasuwanci ko sana’a za ki yi, dage ki yi. Kada ki sake ki zauna haka yadda za ki dogara da iyayen ki ko zawarawan ki.

5: Kada Ki Manta Da Abin Da Ya Kashe Maki Aure:

A kullum ya zama ki na ɗaukar abin da ya kashe maki aure da muhimmanci, ba ki manta da shi ba ki sake yin kuskure.

Wani lokacin maza ne ke ƙirƙiro matsalar da su ke neman hanyar sakin mace. Wasu lokutan mugayen halayen mata ke jawo masu saki. Ko ma dai menene dalilin mutuwar auren ki, kada ki yi sakaci da shi domin kauce wa gaba.

6: Bai Wa Wasu Mazan Dama:

Wasu matan kuskure su ke na ƙin kula wasu mazan da su ke son su da aure bayan auren su ya mutu. Sam, ba duk ba ne maza halayen su ya ke ɗaya ba. Kada ki yi wa wani hukunci da laifin wani. Don haka bai wa wasu mazan dama cikin kiyayewa domin ganin yadda za su taka tasu rawar.

7: Ki Danne Sha’awar Ki:

Kuskuren da wasu mata zawarawa su ke yi shi ne na kasa danne sha’awar su ta jima’i bayan auren su ya mutu. Hakan ya sa duk namijin da ya zo da zancen aure ko soyayya sai kawai ki sakar masa gaban ki. Daga bisani ki kasa samun mai son auren ki na gaskiya. Tabbas, macen da ta riga ta san daɗin jima’i haƙurin rashin sa sai ta jure, sai dai kuma wannan jimirin shi ne mutuncin ta.

8: Ki Yarda Da Sulhu: 

Wasu lokutan bayan an rasa abin da ake da shi ne ake gane muhimmancin sa.

Kada ki ce ba za ki bai wa tsohon mijin ki dama ba idan ya zama ya nemi ku yi sulhu. Ya na iya yiwuwa a wannan karon ya fahimci kuskuren sa kuma zai gyara. Ci gaba da zama da gidan da ki ka saba idan akwai fahimta ya fi zuwa sabon gidan da sabuwar rayuwa za ki soma da su.

9: Ki Yi Don Allah:

Idan za ki koma gidan ki, ki koma saboda Allah da kuma zuciya ɗaya. Hakan idan akwai dalilin da zai hana ki komawa ya zama hujjar da za ki bayar saboda Allah, ba saboda son rai ba.

10: Kada A Yi Maki Tarko Da Yaran Ki:

Tabbas, yara su na da matuƙar shiga rai, musamman wajen uwa. Sai dai kada hakan ne zai sa ki nace ki na son komawa gidan mijin ki. Shi aure ba a zaman sa saboda yara, ana yin sa ne saboda Allah domin ibada ne. Muddin ba zai yiwu a samu gyara a abin da ya jawo maki matsala da mijin ba, idan kin koma saboda yara wahala da matsalar ba gyaruwa za su yi. Su yara ko ki na raye ko ba ki raye za su rayu. Idan uban su ko wata matar ki gidan ta nemi cutar da su damƙa su hannun wanda ya ba ki su, zai kare su. A matsayin ki na mutum ki na son kema ki more rayuwar auren ki ne kamar yadda duk wata mace ke yi, amma ba ki musguna wa kan ki saboda yaran ki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button