HUKUNCIN TSOTSAR FARJIN MACE KO AZZAKARIN NAMJI HARAMUNNE NE??
HUKUNCIN TSOTSAR FARJIN MACE KO AZZAKARIN NAMJI HARAMUNNE NE??

HUKUNCIN TSOTSAR FARJIN MACE KO AZZAKARIN NAMJI HARAMUNNE NE??
Tambaya
:
Shin ko ya halatta ga miji ya tsotsi gaban matarsa ko ita mace ta tsotsi gaban mijinta ko ko kuma ta sha maniyyinsa??
:
Amsa:
:
Asali dai a shari’ance ya halatta mace da miji suyi abin da a ke ƙira da suna (Al-Istimtā’u) wato jin daɗī tsakanin ma’aurata, danhaka ya halatta suji daɗi da junansu yadda sukaga dama, sai dai abin da shari’a ta keɓance tayi hani a kansa, kamar a ce miji ya sadu da matarsa a lokacin da ta ke cikin jinin al-ada ko jini bīƙi, ko kuma miji ya sadu da matarsa ta duburar ta ko rgaduwa da ita lokacin da ta ke yin azumin farilla.
:
Danhaka kenan idan miji ya tsotsi farjin matarsa ko ita mace ta tsotsi azzakarin mijinta Malamai sukace duk ya halatta, saboda hakan zai iya shiga ne cikin Ƙarƙashin hukuncin (Al-Istimta’u) wato jindaɗī tsakanin ma’aurata. Saboda faɗin Aʟʟãн(ﷻ) cewa:
:
”نساؤكم حرث لكم فأتوا حرثكم أني شئتم” (البقرة/الآية223)
MA’ANA:
Matanku Gonakan ku ne, danhaka ku zowa gonakan ku ta inda duk kuka ga dama:
:
A cikin wata ayar kuma Aʟʟaн(ﷻ) Ya ce:
:
”هن لباس لكم وأنتم لباس لهن”
MA’ANA:
(Mātanku) tufāfi ne a gareku, haka kūma (Mazajensu) tufafi ne a garesu.
:
Amma idan ya kasance a na da tabbas ko zato mafi rinjaye gameda cewa yin hakan zai iya haifarwa wani daga cikinsu wata cūta ko kuma ya kasance babu wata cūta da hakan zai haifar sai dai kawai ɗaya daga cikin ma’auratan baya son a yi masa hakan to Malamai sukace bai halatta suyi hakan ba dan gudun kada a cūtar da wanda ba ya so ɗin, sai dai wasu daga cikin Malamai suna ganin duk da cewa yin hakan ba haramun ba ne to amma barinsa shi yafi alkhairi:
:
Amma dangane da magana akan hukuncin cewa idan mace tana tsotsar azzakarin mijinta har ya kai ga yin Inzali (fitar maniyyi) a cikin bakinta, shin ya halatta ta haɗiye wannan ruwan maniyyin ko bai halattaba? Alal-Haƙiƙa a nan Malamai sunyi saɓãni a kan wannan Mas’ala, kuma saɓãnin na su ya ginu ne a kan mas’alar cewa shin maniyyi najasa ne ko ba najasa ba ne? Malaman da suka tafi a kan fahimtar cewa maniyyi najasa ne sukace haramun ne mace ta sha, domin ba ya halatta ga Mutum Musulmi ya ci ko ya sha dukkan abinda ya kasance najasa ne.
:
Sai dai Magana mafi Inganci kamar yadda wasu daga cikin Malamai suka rinjayar itace, cewa maniyyi ba najasa ba ne, to amma sai dai Malamai sukace duk da kasancewar maniyyi abu ne mai tsarki ba najasa ba, sukace bai kamata a ce Mutum ya sha maniyyiba. domin yin hakan yana daga cikin ƙazanta, kamar yadda bai kamata ba a ga Mutum yana shan Majina, duk da cewa majina ba najasa ba ce amma ko shakka babu cewa shanta ɗin ƙazanta ne.
:
※(шαʟʟαнυ-тα’αʟα α’αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи