Advertisement
Trending

Da alamu ƴan Ansaru ne suka kai hari jirgin kasa na Abuja-Kaduna a watan daya gabata.

Da alamu ƴan Ansaru ne suka kai hari jirgin kasa na Abuja-Kaduna a watan daya gabata.

Da alamu ƴan Ansaru ne suka kai hari jirgin kasa na Abuja-Kaduna a watan daya gabata.

Masana da masu nazari kan harkokin tsaro a Yammacin Afirka sun bayyana cewa da alama ‘yan kungiyar Ansaru, wacce ke ikirarin kishin Musulunci, ne suka kai hari kan jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan jiya.

A ranar Laraba ne, wani bidiyo da aka fitar ya nuna wasu daga cikin maharan ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin din makon jiya.

Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna huɗu cikin ‘yan bindigar sanye da kakin sojoji fuskokinsu a rufe a tsaye suna iƙirarin ci gaba da riƙe fasinjojin jirgin ƙasa da suka sace a ƙarshen watan jiya.

Ba a ga fasinjojin a cikin taƙaitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna riƙe da su.

Sun yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya, a wata sanarwa, ta ce fasinja 362 ne a cikin jirgin da aka kai wa hari ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata.

“An tabbatar da cewa fasinjoji 186 da suka shiga jirgin suna cikin koshin lafiya a gidajensu. Sannan akwai karin mutum 14 da su ma yau aka tabbatar sun tsira.

Wayoyin salula na mutum 51 da suka shiga jirgin suna kashe ko kuma ba a iya samun su bayan kiran da aka yi musu tun daga ranar Talata da safe,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa fasinja 22 ne suka ɓata, kamar yadda ‘yan uwansu suka bayyana wa hukumar.

KU KARANTA WANNAN:

Tirƙashi an ceto mata da ƙananan yara 25 da suka ɓata a sahara wanda suke shirin shiga ƙasar Libiya daga ƙasar Niger.

Kalli dalilin dayasa Akeru fewa Mutane Layin wayar salula ga Bidiyo sai kukalla

Innalillahi wa’inna ilalaiyi raji’un anfara kaiwa malam nuru hari akan jawabin sa Harma

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button