Advertisement
Trending

Tirƙashi A gaggauta hukuncin cin zarafin ƴan zanga-zangar End-sars_kungiyar Human Right tayi Tsokaci.

Tirƙashi A gaggauta hukuncin cin zarafin ƴan zanga-zangar End-sars_kungiyar Human Right tayi Tsokaci.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau Litinin, ta bukaci gwamnati da ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar a dauka a kan wadanda aka zarga da aikata laifi.

Kungiyar ta ce, ba zai yiwu a kawar da kai a kan rahoton ba, ba tare da wani abu ya biyo bayan hakan ba a kan wadanda ake zargi da kisa da kuma jikkata masu zanga-zangar.

Ta ce muddin ba a dauki mataki ba a kan shawarwarin kwamitin, hakan zai harzuka wadanda abin ya shafa, tare kuma da karfafa wa jami’an tsaro guiwa kan cin zarafi.

A watan Oktoba na 2020 daruruwan matasa suka kwarara a titunan biranen wasu jihohin Najeriya, suna zanga-zangar neman a rushe rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi da makami, wato SARS, wadda ta yi kaurin suna da cin zarafin jama’a, tare kuma da kawo karshen zaluncin da ‘yan sanda ke yi, abin da ya janyo jami’an tsaro suka mayar da martani da karfin da ya wuce kima.

Daya daga cikin inda lamarin ya fi kamari shi ne na mashigar Lekki da ke Lagos wato Lekki Toll Gate, inda aka bayar da rahoton cewa sojoji da ‘yan sanda sun bude wuta a kan masu zanga-zangar, har suka kasahe tare da jikkata mutane, abin da su kuma suka musanta.

KU KARANTA WANNAN:

Asiri Yayi Shekara Goma Yana ZinaTononh Da ‘Yam Mata Da Sunan Adam A Zango A Shafukan Sada Zumunta

Tonon Asiri Yayi Shekara Goma Yana Zinah Da ‘Yam Mata Da Sunan Adam A Zango A Shafukan Sada Zumunta

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button