Trending
An Harɓe Wannan Matashin A Wujen Zanga-zangar A Saki Waɗanda Suka Ka She Wadda Ta Zagi Manzon Allah (SAW) A Sokoto
An Harɓe Wannan Matashin A Wujen Zanga-zangar A Saki Waɗanda Suka Ka She Wadda Ta Zagi Manzon Allah (SAW) A Sokoto

Yayi Shahada Wajen Kare Martabar Manzon Allah (S.A.W).
Gwamnatin Jihar Sokoto ta saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka gudanar a yau Asabar.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce dokar za ta fara aiki nan take.
An ɗauki matakin ne “saboda dawo da doka da oda a birnin Sokoto da jihar baki ɗaya”, a cewar sanarwar.
Masu zanga-zangar na nemanjami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).