Ya Zama Dole A Ɗauki Mataki Akan Waɗanda Suka Kashe Harira Da ‘Ya’Yanta Huɗu – Abdullahi Amdaz
Ya Zama Dole A Ɗauki Mataki Akan Waɗanda Suka Kashe Harira Da 'Ya'Yanta Huɗu - Abdullahi Amdaz

Biyo Bayan Abunda Ya Faru Na Kisan Wasu Mutane A Hanyar Anambra Wanda Bincike Ya Nuna An Taresu Ne A Hanyar Sannan Akayi Kusu Kisan Gilla, Kamar Yadda Bidiyon Ya Cika Kafafen Sada Zumunta.
Sai Dai Jaruman Kannywood Sun Tayar Da Kayar Baya Wajen Cewa Dole Sai An Kama Wadanda Sukayi Wannan Aiki, Sannan Anzartar Musu Da Hukunchin Daya Dace Dasu.
Abdullahi Amdaz Jarumin Kannywood Ya Wallafa Wani Tsokaci Cikin Fushi A Shafinsa Na Sada Zumunta Wato Facebook Da Instagram Yana Mai Kira Ga Mahukunta Akan Su Duba Wannan Lamari Kuma Suyi Adalchi.
Abdullahi Amdaz Yace
“Kuyi hakuri abokaina yau sakona ba mai
dadi baneshiyasa bazanyi addu’a wa
wani ba ko tausasa masa murya Ya zama dole a dauki mataki ga makasan
Harira Jibril da ‘ya’yanta, tare da sauran mutane shi da, wanda dabbobin
Anambra suka kashe.
sannan dole gwamnati ta biya diyyar wannan rayuka bisa gazawarta, kamar yanda sukai ga dabbar da tayi batanci ga Fiyayyen Halitta.
We need justice for their beautiful souls, Bazamu zura idanu muna kallo rayukanmu su zama abun banza ba,
enough Ils enough muma yan kasa ne,
masu yanci kamar dai sauran dole aji
maganarmu, ada rigimarsu da Gwamnati
suke yanzu ta dawo kan rayukan da
basujiba basu gani ba,
wanda da ace gwamnatin ta dauki mataki hakan bazai faru ba, amma saboda an rainamu harball akace zaa bar shugabansu ya kalla, sun zama threat ga zaman lafiyar kasa amma ana ci gaba da tattalinsu saboda kwadayin siyasar duniya, inbanda dabbanci da gidadanci har wannan mutanen sune ke neman yancin wata karya?, mutanen dake kashe rai akan
burodi?, akan naira dari?.
Inna lillahi wainna ilaihirrajr un ace
mace da juna biyu, ku tareta a ku kashe
akan titi da ya’yanta hudu, hakan bai isa ba saida kuka hada da wasu mutumshida, sannan kuna kiran kanku wayayyu masu neman ‘yanci?, Yo wanne dabbanci ne yakai wannan?,
Wanne zalunci ne yakai wannan?, Kuma munafukan arewa sunyi shiru sunaji?, Babu wanda zaiyi magana saboda son zuciya.
Tsinannu maciya amanar kasa Azzalumai barayin banza barayin wofi, Allah ya isa bazamu yafe ba wallahi, ayita
kashemu kuna sace kudinmu kuna ji
kuna gani.”
Wannan Shine Abunda Jarumin Kannywood Ya Wallafa A Shafinsa Na Instagram Da Facebook Akan Kisan Wannan Mata Da ‘Ya’Yanta Hudu.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Rohoto.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Ku Karanta Wannan Labarin:
Sojojin Najeriya Da Chadi Sun Kashe Manyan Mayakan Boko Haram da Iswap 25.
Ku Karanta Wannan Labarin: