Advertisement
Trending

Bayan Maka Miji a Kotu, Ta Hana Alkali Raba Aurensu, Tana so ya Canza Hali Kawai

Bayan Maka Miji a Kotu, Ta Hana Alkali Raba Aurensu, Tana so ya Canza Hali Kawai

Wata matar aure mai suna Bilkisu
Muhammad a ranar Litinin ta yi kira ga wata kotun shari’a a Kaduna da kada ta tsinke igiyar aurensu da Sirajo Mansur saboda tana son mijinta ya sauke nauyinta da ke kan shi.

Muhammad ya shigar da karar a ranar 23 ga watan Mayu, inda ya ce ya tafi Legas neman aiki amma ya kasa samar da abinci, wurin zama, tufafi da kudin makarantar ‘ya’yan shi.

Vanguard ta ruwaito, ta bukaci kotu da ta sa Mansur ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makaranta.

A martaninsa, Mansur wanda ya samu wakilcin dan uwansa Sulaiman, ya ce wanda ake kara ya umarcesa da ya sanar da kotu cewa ta tsinke igiyar aurensu tunda matarsa ce ta maka shi a gaban kotu.

Ya kara da cewa, ya yi kokarin biyan kudin haya amma mai gidan ya ki karbar kudin saboda ya riga ya bai wa wani dakin.

“A bangaren kudin makaranta, a halin yanzu yara suna rubuta jarabawa ne. Zan biya kudin makaranta bayan an kammala jarabawa,” Inda Alkali Malam Rilwani Kyaudai, ya umarci wanda ake kara da ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makarantar yaran shi.

A Karshe Ya umarci mai gidan hayan da ya hallara a gaban kotu bayan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yuni

inda ita kuma matar ta bukaci da kotu kada ta raba aurenta da mijin nata domin tana son abinta ,kawai tana da bukatar da ya sauke nauyin da kai kansa inda shi kuma dan uwansa ya bukaci da a tsinge igiyar auren nasu

daman de ance hakuri maganin zaman duniya da tabi ta halin sasanto da haka bata faru ba amma tunda abu yaje kotu magana ta bacci saide muce Allah ya daidaita tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button