Advertisement
Trending

Daga Karshe El-Rufa’i Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Apc Ta Zabi Tinubu A Matsayin Dan Takara Shugaban Kasa

Daga Karshe El-Rufa'i Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Apc Ta Zabi Tinubu A Matsayin Dan Takara Shugaban Kasa

Gwamnan jihar Kaduna ya yi bayani game da dalilin da yasa jamiyyar APC ta zabi Asiwaju Bola Tinubu domin takarar shugabancin kasa a 2023 A tattaunawar da aka yi da El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnonin APC daga shiyyar arewa maso yamma sun aminta da Tinubu saboda ya fi kowanne ‘dan takara kasuwa

Fitaccen ‘dan siyasan ya sanar da yadda
shugaba Buhari ya tsaya tsayin daka ba tare da ya zabi ‘dan takarar da ya fi so ba daga cikin masu neman tikitin

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Juma’a, 10 ga Yuni, ya bada bayanin yadda tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jamiyyar APC.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, ya caccaki wadanda suke sukar tikitin takara na musulmi da kuma mataimaki musulmi inda ya kwatanta su da wadanda ba su san abinda su ke yi ba.

Tinubu ya samu kuri’u 1,271 inda ya lallasa ‘yan takara 13 a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC da aka kammala a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni.

El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa
aka zabi Tinubu

A yayin bayyana abubuwan da suka sa Tinubu ya tabbata ‘dan takarar APC a zaben 2023 mai gabatowa, El-Rufai ya ce gwamnonin arewa maso yamma sun gana kafin zaben fidda gwanin kuma sun yanke hukuncin goyon bayan Tinubu saboda shi ne ‘dan takara da yafi kowanne farin jini da masoya.

masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci sannan idan wannan karanka na farko da ka danna mana alamar kararrawar sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button