NAHCON ta canja kamfanin da zai jigilar alhazan Kano da ga Azman Air zuwa Max Air
NAHCON ta canja kamfanin da zai jigilar alhazan Kano da ga Azman Air zuwa Max Air


Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta bada tabbacin cewa kamfanin jirgin sama na Max Air ne zai yi jigilar maniyatan jihar zuwa Saudi Arebiya domin gudanar da Hajjin 2022.
Hajj Reporters ta rawaito cewa matakin NAHCON na sahalewa Azman Air ya yi jigilar alhazan Kano ya gamu da tirjiya, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Sai dai kuma Shugaban Hukumar Alhzai ta Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta ya musanta cewa hukumar ta ƙi amincewa da kamfanin Azman, inda ya tabbatar da cewa basu taɓa ƙalla alaƙar aiki a junansu ba.
Sai dai kuma ya ce hukumar na tattaunawa da NAHCON kan kamfanin da zai yi jigilar alhazai na Kano.
A wani taron manema labarai a yau Lahadi, Dambatta ya ce sun kammala tattauanawa da NAHCON, inda suka tsayar da matsayar kamfanin jirgin sama na Max Air shi ne zai yi jigilar maniyatan jihar Kano zuwa kasa mai tsarki.
Yace dama rashin kammala tattauanawa da hukumar NAHCON ne ya hana hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta sanar da kamfanin da zai yi jigilar maniyatan jihar.
Babban sakataren ya kuma ce zasu fara tantance lafiya maniyatan su a gobe litinin domin tabbatar da cewa ba’a sami alhazai masu dauke da cutar murar burrai da cutar korona ba.
Ya bada tabbacin kowanne lokaci daga yanzu za’a fara jigilar maniyatan jihar Kano zuwa kasa mai tsarki.
KU KARANTA WANNAN:
Hanya Mai Sauki Da Namiji Zai Gamsar Da Mu Yaya Mata – zuwairiyya
Kallo cikakken video Shagalin Bikin auren Ummi Rahab da Lilin Baba Hamisu breaker, Ado Gwanja
Subhanillahi Yadda Yan ISWAP Suka Kashen Mutane Da Dama Tare Da Garkuwa Da Wasu A Borno
Shekara 5 Aka Bawa Auren Lilin Baba Da Ummi Rahab Sakinta Zaiyi Yan TikTok – Duniyar Kannywood
Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar mungode.