Trending

Majalisar dattijai ta amince da mutanen da Buhari ke son naɗawa Ministoci

Majalisar dattijai ta amince da mutanen da Buhari ke son naɗawa Ministoci

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da sabbin ministoci bakwai da shugaba Muhammadu Buhari ya tura ma ta domin tabbatar da naɗinsu.

An tabbatar da naɗin ne bayan zaman tantace su da majalisar ta yi a zamanta na wannan Larabar.

Yayinda wasu daga cikin sabbin ministocin, musamman tsohon ɗan majalisa, da aka bukaci su yi gaisuwar majalisa su wuce, wasu daga cikinsu an tsare su da tambayoyi kan abubuwan da ya shafi kasa.

Shugaba Buhari, a wata wasika da ya aikewa majalisa mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuni, 2022, ya bukaci majalisar ta amince da naɗinsa.

Ya ce neman bukatar amincewa da naɗin ya yi daidai da tanadin kudin tsarin mulki sashi na 147(2) na kudin tsarin mulkin shekara ta 1999 na Tarayyar Najeriya, da aka yiwa kwaskwarima.

Ministocin da aka tabbatar da naɗin nasu sun haɗa da: Henry Ikechukwu Ikoh – daga Abia; Umana Okon Umana – daga Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama- daga Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah – daga Imo.

Sauran su ne Umar Ibrahim El-Yakub – daga Kano; Ademola Adewole Adegoroye – daga Ondo; da Odum Udi – daga Rivers.

Bam ya tashi a wurare da dama a Ethiopia
‘Yansanda a Ethiopia sun ce an samu tashin bam a wurare hudu a birnin Bahir Dar na arewacin kasar.

Babu dai wani bayani kan ko an samu hasarar rayukka ko jikkata.

Wani kakakin ‘yansandan ya ce an kama mutane shida da ake tuhuma.

Zaman tankiya ya karu a yankin Amhara a baya-bayan nan, bayan wani samame da hukumomin suka kai kan kungiyoyin mayaka inda aka kama dubban mutane.

An yi ta zanga-zangar kin-jinin-gwamnati a wannan watan sakamakon kashe ‘yan kabilar Amhara fiye da 200 a yakin Oromia mai makwabtaka.

Masu aiko da rahotanni sun ce tashin bama-baman wata alama ce ta karuwar zaman dar-dar a Ethiopia wadda ke fama da tashe-tashe hankula iri daban-daban.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button