Trending

Shirin Fina-Finai Dasuka Kawo Lalacewa Tarbiyar Hausawa – Masu Dogon Zango

Shirin Fina-Finai Dasuka Kawo Lalacewa Tarbiyar Hausawa - Masu Dogon Zango

Acikin Watannin Da Suke Wuce Ne Aka Samu Bullar Wasu Fina-finai Masu Dogon Zango Wadanda Basu Da Amfani Wajen Bayyanasu Biyo Bayan Saba Al’adar Hausawa Da Sukayi A Wasan Kwaikwayo.

Akwai Wasu Fina-finai Da Bullar Tallarsu Ta Janyo Hankalin Jama’a Ciki Harda Wasu Daga Cikin Malaman Addini, Yadda Suka Tofah Albarkacin Bakinsu Akan Haka.

Fina-finan Da Sunansu Ba A Boye Yake Ba, Tun Bayan Bullarsu: Bintalo,Makaranta Da Kuma Wani Sabo Wanda Sashe Ne Na Cikin Daukan Film Din Ya Bayyana Mai Suna ‘Yababulu‘.

Amma Fina-Finan Dasuka Dauki Hankulan Jama’a Babu Kamar Bintalo Wanda Shine Film Din Dayake Bayyana Cin Amanar Rayuwar Aure, Yadda Mace Take Gayyatowa Maza Gidanta Suna Biyanta Kudi Suyi Lalata Da Ita, Na Biyu Kuma Shine Makaranta Wanda Yake Bayyana Kalaman Jima’i Da Kuma Wayewar Zamani A Makarantun Yanzu Musammn A Jami’a.

Acikin Wadannan Fina-finai Guda Biyu Bai Kamata Yara Kanana Suna Kallarsu Ba, Duba Da Yawanchi Ana Samun Masu Yin Koyi Da Abunda Fina-finai Suke Koyarwa A Yanzu, Saboda Lalacewar Tarbiyya.

Ga Cikakken Bidiyon Bayanin Da Mukayi Bincike Akan Wadannan Fina-finai Sai Ku Kalla A Manhajar YouTube.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wadannan fina-finai Guda Biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button