Trending
‘Ashe Gurgune Da Ƙafar Ƙarfe Yake Zuwa Hira Wajena’ – Budurwa Ta Koka
'Ashe Gurgune Da Ƙafar Ƙarfe Yake Zuwa Hira Wajena' - Budurwa Ta Koka

Wata Kyakkyawar Matashiyar Amarya Ta Gane Cewa Angonta Gurgu Ne Bayan Aurensu, Ashe Da Ƙafafun ‘Acuci Mata’ Ya Dinga Zuwa Fira
Amarya Bora da mijinta mai suna Joda sun ɗauki tsawon lokaci suna soyayya amma bai taɓa sanar da ita ƙafafun roba ba ne da shi don gudun kada ta fasa aurensa.
Hakan ya samo asali ne saboda yadda mata ke rabuwa da shi da zaran sun fahimci naƙasar da ke tattare da shi.
Koda ta sani bayan aurensu bata watsar da mijin nata ba inda ta rungume shi hannu bibbiyu.
A Wani Labarin Kuma Na Daban
Sojoji Sun Afkawa ‘Yan Shi’a Masu Komawa Gida Bayan Gama Muzahara