Advertisement
Trending

Ali Nuhu Yakai Dansa Ahmad Ali Nuhu Ingila Domin Kwaraiwa A Wasan Kwallon Kafa

Ali Nuhu Yakai Dansa Ahmad Ali Nuhu Ingila Domin Kwaraiwa A Wasan Kwallon Kafa

Sanannen jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana hotunan zabgegen saurayin ‘dan shi, Ahmad, wanda ke wasan kwallon kafa a Ingila.

Mahaifin mai cike da alfahari da ‘dan shi, yayi masa fatan alheri yayin da ya wallafa hoton matashin yana sanar da cewa yana shirin fita wasa ne

Ali Nuhu ya wallafa hoton matashi Ahmad a shafinsa na Instagram kuma kara da bayanai masu kara karfin guiwa a wasan da zasu buga Danna Kan suna ali nuhu domin ganin wallafawar realalinuhu

 

Ma’abota amfani da kara sada zumuntar
zamanin na duniya sun dinga tururuwar yin tsokaci karkashin wallafar Ali Nuhu kan’dan shi tare da rubuta kalaman sam barka, Kamar yadda shafin Dalatopnews.com Suka tattaro

TSOKACI

Deejay_kz.: “Gwarzon duniya a nan gaba.”

Eeshaq678: “Zaka samu alfahari wata rana da izinin Ubangiji.”

Zuwairatummumaryam: “Barakallahu MashaAllah, wannan yaron na girma da hanzari. Ina fatan ka daukaka a duk abinda ka saka gaba a rayuwarka. Amin.”

Tahansy: “A bayyane kamanninku suke. Karin ni’ima ga iyalanka Ya Rabbi.”

Ibrokhan20: “Ina fatan zai yi nasarar zama fitaccen ‘dan kwallo.”

Aleemlah: “Wannan yaron ya yi matukar kama da mahaifinsa, hazakarsu a jini take, nan babu dadewa yan mata zasu fara bibiyarsa.”

Masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci sanna muna da bukatar da ku danna mana alamar kararrawar sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button