Advertisement
Trending

Anyi Nasarar Kama Wata Mata Mai Safarar Yara Daga Maiduguri In Ta Kwashi Yara Uku Zata Jihar Lagos

Anyi Nasarar Kama Wata Mata Mai Safarar Yara Daga Maiduguri In Ta Kwashi Yara Uku Zata Jihar Lagos

Kamar yadda kuka sani a wannan lokacin da muke ciki yawan satar yara tare da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare inda ko ma’aikatan tsaro suma basu tsira ba

Hakan ne yasa aka tsaneta bincike domib dakile wannan ta’addanchin a kasa baki daya inda akayi nasarar cafke wata mata dake safarar yara daga maiduguri zuwa wata jihar kamar yadda shafin rariya suka rawaito

An Kama Wata Mai Safarar Yara A Maiduguri, Inda Ta Kwashi Yara Uku Za Ta Kai Su Jihar Lagos

An kama wannan mata mai suna Nsa Heneswa a tashar Borno Express dake Maiduguri yayin da take kokarin tafiya jihar Lagos da yara uku da ta sace.

A bayanin da ta yi tace dubu dari biyar Lady B dake Victoria island a Lagos ta biya ta domin ta yi wannan aikin. Kuma wannan ne karon farko da ta yi nasarar samun yara, sannan kuma ta ce akwai wata nurse a Maiduguri Specialist Hospital da take taimaka mata akan wannan aika-aikan.

Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu Allah ka zaunar da kasar mu lafiya.

Daga Yahaya Yakubu Alasan Barbaji

Masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen muna tsokaci sannan muna da bukatar da ku danna mana alamar kararrawar sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button