Manoman ƙasar Najeriya na kokawa kan karancin takin zamani.

Manoman ƙasar Najeriya na kokawa kan karancin takin zamani.

Manoma a Najeriya na ci gaba da kokawa game da karancin taki yayin da damina ta yi nisa.

Manoman sun ce taki nau’in Yuriya, wanda shuka ke buƙata a daidai wannan lokaci da ake marka-marka, ya yi wahala a kasuwa.

Dillalan takin dai na danganta ƙarancinsa a kasuwa da kamfanonin samar da shi, inda suke cewa ko sun biya kuɗi, ba sa samu.

Manoman musamman na arewacin Najeriya na cewa a yanzu ko da kudinka zai yi wahala mutum ya samu takin a kasuwa.

Manoman shinkafa da masara da dawa na matukar bukatar takin domin ya taimaka wa amfanin gonar ya habaka.

Alhaji Idris Mai Unguwa, shi ne shugaban kungiyar manoma ta Jihar Jigawa, kuma ya shaida mana cewa tun da watan Agusta ya kama taki nau’in Yuriya ya soma wahala.

Ya bayyana cewa ko da manomi ya ci sa’a ya samu takin, farashinsa ya tashi matuƙa.

Haka kuma ya ce yanzu ne lokacin ruwa da ya kamata a ce an samu takin an saka, idan ba haka ba kuwa ba shi da wani amfani nan gaba.

Ba iyakar manoman Jihar Jigawa ba ne ke kokawa da karancin takin samfurin Yuriya ba, sauran jihohin arewacin kasar ma haka lamarin yake, sai dai wasu jihohin kari a kan wannan matsalar, takunkumin da aka sanya na hana sayar da Yuriya din, saboda matsalar tsaro na matuƙar shafar su.

Jihohin sun haɗa da Gombe da Yobe da Borno da Adamawa da Taraba.

Alhaji Modibo Sadiq Nafada shi ne shugaban kungiyar manoma na jihar Gombe kuma ya shaida mana, cewa kamfanoni uku ne kacal ke wadatar da Najeriya da Yuriya inda ya ce matsalar Yuriya matsala ce da ta shafi Najeriya baki ɗaya.

Ya bayyana cewa wannan matsala ta sa an koma amfani da kashin dabbobi da juji da sauran abubuwan da aka baro a baya inda ya ce manoma ba su jin daɗin wannan lamari.

Sai dai dillalan takin sun bayyana cewa su kansu sun shiga halin rashin tabbas saboda sun shigar da kudi a kamfanonin samar da takin, amma a cewar Alhaji Haro Shehu, wani dillali a jihar Jigawa, har yanzu ba su samu takin ba.

Duk kokarin da mobile media crew ta yi domin ji daga hukumomi hakan bai yiwu ba.

To sai dai wata majiya da ke kusa da shugaban kwamitin shugaban kasa kan harkokin taki, da kuma gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar, ta ce gwamnan ya zare hannunsa daga sabgar takin, tun shekaru biyu da suka gabata, saboda wasu tsare-tsare da wasu jami’an gwamnati suka bullo da su kuma ya yi gargadin cewa za su iya haifar da wannan matsalar da ake ciki yanzu.

Amma a cewar majiyar an yi biris da shawarar da ya bayar, al’amarin da ya sa ya kakkaɓe hannunsa duk da cewar bai ayyana sauka daga shugabancin kwamitin ba.

KU KARANTA WANNAN:

Tofa: An Tsinci Gawar Mace Da Namiji, Kuma Dukkansu Tsirara A Cikin Wani Kango A Garin Suleja.

 

Anyi Nasarar Kama Wata Mata Mai Safarar Yara Daga Maiduguri In Ta Kwashi Yara Uku Zata Jihar Lagos

 

Subhanillahi Yadda Da Da Uba Suka Mutu Yayi Yashe Rijiya A Jihar Kano

Kada kumanta kudanna mana alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button