Trending

Rundunar ƴan sandan jihar Venue sun shiga kama bokaye da matsafan d a  suka addabi jihar.

Rundunar ƴan sandan jihar Venue sun shiga kama bokaye da matsafan d a  suka addabi jihar.

Yan sandan jihar Benue a ranar Talata sun tabbatar da kama wasu mutane 30 da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar asiri a garin Gboko da ke karamar hukumar Gboko a jihar Benue.

Daily Trust ta tattaro cewa mutane uku ne ake zargin an kashe a rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar asiri da ya faru a karshen mako.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Binuwai, SP Catherine Anene, a ranar Talata da yamma, ta shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa an kawo mutanen 30 da aka kama a Makurdi.

“An kama mutane 30 da ake zargi, ana kawo su Makurdi yayin da muke magana don haka za a samu karin bayani daga baya,” in ji Anene.

Sai dai an samu labarin cewa tun da farko mazauna yankin sun yi tururuwa domin tsira da rayukansu bayan da ‘yan kungiyar suka tayar da tarzoma a yankin yayin da suke fafatawa da junan su da muggan makamai.

Wani ganau ya ce matakin gaggawa na shugaban karamar hukumar Gboko, Issac Mtom, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro a yankin ya sa aka shawo kan lamarin.

A wata sanarwa da Mtom ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Bright Antyo, wanda ya tabbatar da mutuwar mutane uku a rikicin, ya bukaci a kwantar da hankula.

“Shugaban karamar hukumar Gboko ya yi kira ga daukacin mazauna garin na Gboko da su kwantar da hankalinsu tare da sanya ido kan rikicin da ake kyautata zaton ya barke tsakanin kungiyoyin asiri guda biyu.”

“Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake samun rahoton hare-haren da kungiyoyi suka kai wadanda ake zargin sun yi sanadiyyar mutuwar wasu matasa uku. Ya nanata rashin hakurin sa ga duk wani nau’i na tashin hankali ko ayyukan da ke iya haifar da hargitsi da tabarbarewar zaman lafiya da tsaron karamar hukumar Gboko.”

“Ya kuma yi kira ga matasa da su guji ayyukan daba domin duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a gaban shari’a,” inji sanarwar.

KU KARANTA WANNAN:

Masha Allah , Kalli Videon Wasu Tsofaffi Mata Da Miji Masu Shekaru 162 , Suna Raira Karatun Alkur’ani.

Dalilin Dayasa Kotu Zata Kama Safara’u – Ado Gwanja – Mr442 – Murja TikTok Da Sauransu

 

Tofa! Ikon allah kalli abun mamaki a kabarin wani bawan Allah alumma sun shiga tattayin su.

Kada kumanta kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button