Duniya Tazo Karshe: Yadda Iyaye Maza Suke Barin Matansu Don Komawa Kan ‘Ya’ya Mata Da Suka Haifa Innalilahi wainna ilaihir raji’un
Duniya Tazo Karshe: Yadda Iyaye Maza Suke Barin Matansu Don Komawa Kan ‘Ya’ya Mata Da Suka Haifa Innalilahi wainna ilaihir raji'un

Rahotanni sun tabbatar da cewa, a cikin shekara biyu da suka wuce,iyaye 34 ne suka yi wa ‘ya’yan cikinsu 48 fyade, a cikin wasu bayanai da jaridar ‘Daily Trust’ ta ranar Lahadi ta tattara.
A wani bincike wanda majiyarmu jaridar Leadership tayi Jihar Legas ita ke kan gaba da mutum 11 sai Ondo 5, sai Ekiti 4, sai Kwara 3, sai Ogun ita ma 3, sannan sai Abiya da Anambura da Kano da Delta da Osun da Katsina da Edo da kuma Kuros Riba wadanda kuma kowannensu ke da daya.
Kamar yadda kididdigar ta nuan,daga cikin matsalolin 46 da suka faru, daya daga cikinsu jaririya ce, hudu kuma ‘yan kananan yara ne,sauran kuma kananan ‘yan mata guda 15.
Labari na baya-bayan nan da aka samu shi ne, a cikin watan Agusta, 2022, shi ne, na wani mai gadi mai kimanin shekara 55, mai suna Arowolo Ayodeji, ya yi wa ‘yarsa mai kimanin shekara 19 fyade a garin Ipoti da ke jihar Ekiti.
Da aka tambayi mahaifin yarinyar ko mai ya sa ya yi wannan danyrn aik? Sai ya ce, sharrin Shaidan ne, “Ba aikina ba ne.”
Mai magana da yawun jami’an tsaro na Sibil Difens (NSCDC) Olasunkanmi Ayeni, ya bayyana cewa, mutumin ya fara tursasa wa yarinyar tun tana ‘yar shekara bakwai.
“Wato zuwa yanzu ya shafe shekara biyu yana aikata wannan laifin ke nan,” In ji Mista Ayeni.
Ranar 19, ga watan Fabarairu 2022, haka kuma wani mutum mai shekara 28, mai suna Audu Dare, wanda ya yi wa ‘yarsa fyade mai shekara 6, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta, sakamakon haka aka tsare shi a Ado Ekiti.
Matar da Dare ya ci gaba da bibiya wata mai suna Eniola Aina, wadda ta ce sun taba yin aure a shekarun baya, kuma har ma sun haifi da namiji amma sai suka rabu, shekara hudu da suka wuce sakamakon wasu munanan halayensa.
“Bayan rabuwarmu, wata rana, sai ya zo gidana da ke garin Ilawe Ekiti ya ce, zai karbi ‘yarsa, ni kuma na ce, ba zan ba shi ba, sai ya dawo da misalin karfe 12 na dare ya sace ta”.
“Bayan ‘yan kwanaki kadan sai yarinya ta fara kukan ciwon kai sannan kuma ta ce mafitsararta na yi mata zafi. Nan da nan aka kai ta wani asibiti da ke kusa da su, a nan ne ta gaya min cewa, babanta ya yi mata fyade wanda kuma hakan ta yi sanadiyyar mutuwarta.”