Shin Da Gaske Ne Harkar Film ce ta làlata Rayuwar Fati Shu’uma

Shin Da Gaske Ne Harkar Film ce ta lalata Rayuwar Fati Shu’uma
Kamar yadda kuka sani duk wani ma’abocin kallon fina-finan kannywood wato hausa fim dole sai yasan jaruma Fati Shu’uma saboda tana daga daya a cikin manyan kannywood kafin tauraruwarta ta kwanta sannan ta taka rawar gani sosai sannan a bangaren da ake saka ta a fim dole ka kalli duk fim din data fito.

A yan kwanakin nan wasu bidiyo da hotuna nata sun bayyana wanda mutane suke yadawa a matsayin itace a ciki sannan suna cewa rayuwarta ta lalace bayan daina saka ta a fim ma’ana bayan tauraruwar ta ta daina haskawa.

Mutane da yawa suna yadawa a soshiyal midiya wato kafafen sada zumuntarsu na zamani. Sannan mutane da yawa za’a iya cewa kashi tamanin cikin dari sun yarda da rayuwar wannan jaruma ta lalace duba da yadda tayi shiga wacce bata dace ba a cikin bidyo din da hotunan.

Ganin haryanzu wannan jaruma bata ce komai ba gane da zargij da mutane sukeyi. 24blog ta gudanar da bincike ta gano wannan zargi da ake yiwa wannan jaruma ba gaskiya bane hasali ma hotunan da bidiyon da ake yadawa ta kusa shekaru ukku da yinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button