Trending

Cin Amana Wannan Cin Amana Dame Yayi Kama, Wannan Mutumen Bashida Imani, Ɗan Maƙwabcin Sa

Cin Amana Wannan Cin Amana Dame Yayi Kama, Wannan Mutumen Bashida Imani, Ɗan Maƙwabcin Sa

Cin Amana: Wannan Cin Amana Dame Yayi Kama, Wannan Mutumen Bashida Imani, Ɗan Maƙwabcin Sa.

MATSALAR TSARO

 

Dangi kuzo gareni a yau zani baku zance

Akan batun tsaron nan da ya barmu yau a zauce

Yau ba tsumi garemu, dabara ko sai a zance

Domin jinin mutanenmu ake ta kyalayarwa

 

Ɓarnar tana yawa; mu faɗi babu kauce-kauce

Ana ta haihuwar guzuma, ɗa, uwa a kwance

Kullum muna tunanin ya ranmu zai kasance

Idan sukai nufin su kashe babu mai hanawa

 

Birni da ƙauyuka, hantsi har zuwa maraice

Idan suna kisa har mara lafiya na kwance

Sun ƙona dukiyoyi, sun barmu mun talauce

Har soja ma gudunsu suke babu me tsayawa

 

Waɗansu sun tare hanya sunyi kwance-kwance

Satar mutum suke a biya, anƙi rai su fauce

Dangi su saida duk kadarorinsu har da rance

Su fanshi ɗan’uwansu a hannunsu ba tsayawa

 

Dukkan ta’annatin da suke nabi na karance

Batun ana tayin galaba kansu duk bula ce

Duk mai faɗin akwai nasara barshi zai kurumce

Ƙarya fure take bata ɗiya irin na maiwa.

 

Idan kana waya kayi katari da masu kwace

Ka basu ko su far maka sara su barka kwance

Polis batun tracking a wajensu ja’iba ce

Sai dai ka barwa Allah shi ne yake mayarwa

 

A Borno ko masifar sai dai kawai kwatance

Har sansanin gudun hijarar tasu ya ƙazance

Fyaɗe da karuwanci da bara da cuce-cuce

Sauƙi ko sai wajen Allah Rabbi mai iyawa

 

Wani ɗan’uwa yace Nasiru ai kawai ka mance

Wahala tasa na ƙyale ‘yata a karuwance

Sai tabi ‘yan maza sun ɗauketa sun kaɗaice

Sannan mu samu lomar ci ko abin ciyarwa

 

Ya sake ce dani matata fa ta makance

‘Ya’ya maza guda uku ta huɗunsu ‘yar macen ce

Biyu sun ɓatan dabo an nemesu babu dace

Sai addu’a nake gun Allahu ba gazawa

 

Kaiconmu ‘yan’uwa wai ko shirunmu fa’ida ce?

Muna gani ana sara mutum kamar itace

Daba a lungunanmu da gayunga masu ƙwace

Tsoro ya samu ko tari babu me iyawa

 

Batun tsaron ƙasar nan wallahi yaudara ce

Na kasa gane shin wai koma manaƙisa ce?

Ina janar janar ɗin ko duk uwar ɗarin ce?

Sai mai tarewa oga hanya kuke kashewa?

 

Kai ɗan’uwa tsaya kaji karma ka sakankance

Ba mu a zuciyar mai mulkinmu karka mance

Ka nemi kariyar Allah safe har maraice

Shi ne kawai yake hana azzalumai sakewa

 

Ko ni da nai rubutun nan zuci na amince

Ba dan tsaron Ilahu ba da na daɗe a kwance

Ina su Dadiyata yau babu sai a zance

Sai ko da mun tuno su hawayenmu suyi zubowa

 

Kana gani fa har ‘ya’yayenmu an farauce

An kaisu can kudanci an sasu yin barance

An canja harsuna; addininsu anyi ƙwace

Batun a ɗau mataki kuwa babu mai kulawa

 

Wani shugaba cikinmu da yaji zuciyarsa kwance

Yace da duniya ai sakaci muke a sace-

‘Ya’yanmu, da da iko ɗauremu zai a mance

Ai dolema a rainamu a dinka hallakarwa

 

Zan cigaba, insha Allahu

©Nasir Ahmad Sadiq

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button