Trending

Yan Uwa Ayi Hattara: Kalli Sabuwar Hanyar Da Barayi Suka Shigo Da Ita Domin Cutar Al’umma

Yan Uwa Ayi Hattara: Kalli Sabuwar Hanyar Da Barayi Suka Shigo Da Ita Domin Cutar Al’umma

Barayi sun bige da barci bayan sun tattar kayan sata a gidan wata tsohuwa

 

“Wasu matasa barayi, Sun Shiga Gidan Wata Tsohohuwa Bayan Sun Gama Kwashe Kaya Barci Ya Dauke Su Nan Take.”

 

“Majiyar Alfijir Hausa ya shaidawa jaridar cewa! Daman tsohuwar an dade anai mata sata a cikin gidanta, wani lokaci tsohuwar ta tsayu cikin dare tana fadawa Allah; da nufin Allah ya tona mata asirin masu yi mata wannan aika-aikan, a karshe dai Allah ya tona asirin su, bayan da barayin suka kamala kwashe mata kaya kaf.

 

“Hakan ya kara bude wata sabon fai-fai ne, ita kuma tsohuwar tana can tana sharara barci, nan take dai barayin sai suka bige da barci, barci kuma mai nauyin gaske, Wanda har sai da tsohuwar ta tashi da nufin za ta zaga ban daki aikuwa tsohuwar ta yi arba da wadannan barayin kwance share-share kowa da abinda ya kwashe gaban shi”

 

“Alfijir Hausa ya kara samun wasu bayanai daga majiyoyi cewa! Tsohuwar ‘Yar gata Ce a wurin Dan cikinta, inda Dan nata ya gwangwajeta da kayan alatu ta zamani, kama daga abin kallo ta zamani, rediyo, firiza da dai sauran nau’oin kayan wuta na ababdn more rayuwa”

 

Bisani sai tsohuwar taje tataso wani jikanta dake kwana a gidan daya zo yaga abin mamaki, inda nan take jikan nata ya kakkaftawa wadannan barayin wadannan hotunan da mai karatu yake kallo.

 

“Wannan al’amarin ya faru ne a wani gari da ake kira da BA’ASI ta jahar Oyo a tarayyar Najeriya”

 

“Shin ko me zaku ce ?.”
Abin Da Ya Sa Arewacin Najeriya Ya Fi Kudu Talauci – Masana

Yan Najeriya ciki har da masana tattalin arziƙi na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta fitar, da ke nuna cewa mutum miliyan 133 ko kuma kashi 63 cikin 100 na ‘yan ƙasar ne ke fama da talauci.

Rahoton ya ce kashi 65 cikin 100 na matalautan Najeriya wato mutum miliyan 86, suna zaune ne a arewa.

Rahoton ya bayyana Ondo a matsayin jihar da ta fi ƙarancin matalauta da kashi 27 cikin 100,

Yayin da Sakkwato ta fi yawan matalauta inda kashi 91 na ‘yan jihar ke fama da talauci.

Masana dai na cewa akwai tazara mai karfi tsakanin masu arziki da talaka, duk da cewa kasar mai arziki ce talakawanta sun fi yawa.

Sai dai ko mene ne dalilin da ya sa talauci ke karuwa a arewa?

Farfesa Kabiru Isa Dandago, masanin tattalin arziƙi a Jami’ar Bayero da ke Kano ya shaidawa BBC cewa Najeriya na cikin wani yanayi saboda kaso mai yawa na tattalin arzikin kasar na hannun mutane tsiraru.

Ya ce kididdiga da aka fitar a kan hanya take, saboda gwamnatocin da ake tayi a kasar tsawon shekara da shekaru sun gaza fito da hanyoyin tsuke tazara tsakanin masu hali da talakawa.

Rahotan ya nuna cewa mata da yara a arewacin Najeriya ne suka fi talauci, saboda rashin ba su damammaki na jari da kananan sana’o’i da ilimin da ya kamata, a cewar masani.

Ya ce a arewacin Najeriya ba a samun wadatuwar mutanen da ke shiga harkokin noma da kere-kere da fanin yawo ido da masana’antu.

Wadannan su ne dalilan da suka sa talauci da fatara da yunwa ke yawaita a arewa.

Farfesa Kabiru ya ce mafita shi ne gwamnati ta sake duba batun Rashawa a nemi hanyoyin rageta ko da kawar da ita a yanzu mai wahala ne.

Sannan akwai bukatar bijiro ko kwadaita masu zuwa yawon bude ido da jari na gida da waje, a shiga harkokin da za su kawo hada-hadar tattalin arziki.

Ya ce Najeriya tana da dukiya amma babu dabarun wadatuwar ayyuka, dole sai an nemi taimako daga waje.

Sannan ya ce harkar ilimi na fuskantar koma baya, dole ne a inganta wannan fanin a saye ruhin mutane ta wannan fanin kafin a ga sauyin da ake fata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button