Advertisement

Yadda zaku hada maganin karin kuzari da gajiya yayin saduwa da iyalin ku

Yadda zaku hada maganin karin kuzari da gajiya yayin saduwa da iyalin ku

Ina Mata da maza wadanda suke da bukatar Karin kuzari kuma basa jin Dadi saduwa to ga wannan hadin sai a jaraba za’aji dadin sa da yardan Allah.

1. Dabino
2. Madara na ruwa ko nono.
3. Zuma
4. Citta

Yadda za’a hada, a sami dabino mai kyau a tabbatar an gyara shi sai a samo madaran nan ko nono.

Sai ki zuba dabino a cikin madaran ki bar shi yayi tsawon awa goma ko ki yi hadin da daddare domin ya jiku da safe sai ki markada sai ki zuba Zuma a ciki da citta sai ki rinka sha safe da yamma.

Da yawa mutane suna neman magani ne,amma sai su tsallake asalin magani su tafi neman wani abu daba bisa rashin sani.

A yau insha Allahu zan sanar daku 2 daga cikin amfanin shan Garin kaninfari da madara ta ruwa

1. Yana magance matsalar saurin kawowa

Matsalar saurin kawowa matsala ce da take damun mafi yawan magidan ta a wannan lokaci musamman ma wadan da basu da manyan shekaru,wanda hakan a tare dasu babbar illa ce da kuma barazana a zamantakewar su da abokan zaman su.

2. Matsalar infection.

Infection wanda aka fi kira da sanyin mara,shima yana daga cikin ciwokan dake dakun jama’a mata da maza, yan mata, da zawarawa.

Shin ta wacce hanya zaa iya magance wadannan matsaloli da kaninfari ?

Za’a nemi :

1. Garin kaninfari
2. Madara ta ruwa

Za’a samu garin kaninfari rabin karamin chokali a zuba a ciki karamin kofi na madara ta ruwa a juya sosai sannan ana sha sau daya a rana har na tsawon kwanaki 7, ma’ana sati daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button