Trending

Abunda Ya Kamata Ku Sani Game Da Amfanin Tafarnuwar (5) Ga Lafiyar ‘Ya Mace

Abunda Ya Kamata Ku Sani Game Da Amfanin Tafarnuwar (5) Ga Lafiyar 'Ya Mace

Amfanin Tafarnuwa Biyar Da Yakamata Ku Sani Ga Lafiyar Mace Sune Kamar Haka:

1.SHAYAR DA KARAMIN YARO: ldan mai shayarwa tana so nononta ya wadaci jaririnta kuma kada ciwo ya kama nonon nata sai ta ci dabino bakwai sannan ta sha man tafarnuwa cokali daya.

2. CIWON CIKI & KULLEWAR MARA: Bayan haihuwa, sai a sami ruwa mai dumi kofi daya a zuba man cikin cokalin shayi daya sai ta sha ta yi haka kwana uku.

3. HAILA,FITSARI,JININ BIKI: Wanda ke yin ba haya da kyar ko fitsari da kyar ko wajen fitar jinin haila sai an sha wuya ko jinin biki, sai ta rika shan karamanin cokali daya da safe daya da rana daya da dare, zata warke sai dai budurwar da take da budurcinta Idan tafiya yawan yin amfani da man tafarnuwa zata rasa budurcinta.

4. MUHIMMIYAR FAIDA: Idan mace tana bukatar maniyyinta ya yawaita sai ta sami madarar saniya kofi daya ta zuba man ta sha kofi daya da safe, kofi daya da dare, matar da tayi haka zata bai wa mijinta sha’awa da mamaki matuka.

5. FARJINTA YA TSUKE DAN KARAMI: Matar kuma da take so farjinta ya zama a tsuke dan karami, daidai yadda zata gamsar da mijinta yadda idan ya sadu da ita ba zai sake tunanin wata ba. 5ai ta sami “man zaitun ” rabin-rabi na cikin cokalin shayi daya, sai ta hada da cikin cokali daya na man tafarnuwa taa gauraya, sannan sai ta tsoma da auduga mai kyau tasa a gabanta, bayan awa 3 sai ta cire ta yar da audugar tayi haka sau hudu ko sau biyar idan tayi haka gabanta zai dawo daidai da na budurwa wadda wani bai taba kusantarta ba amma a tsuke wa ba budurci ba.

Allah Yasa Mu Dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button