Ingataccen Maganin Karin Ruwan Maniyyi Da Kuma Saurin Kawowar Yayin Jima’i Da Iyali
Ingataccen Maganin Karin Ruwan Maniyyi Da Kuma Saurin Kawowar Yayin Jima'i Da Iyali

Maganin Qarancin Ruwan Maniyi A Cikin Sauki:
Abubuwan Da za a tanada
1.Dabino
2. Madara (peak milk)
Za a Nemo dabino Mai laushi misalin Rabin kwano. Da qaramin gwangon madara, a cire diyan dabinon a zuba ruwa a Kofi Sai a jiqa ya kwana.
Da safe a tace shi sannan a zuba Rabin gwangon madara a gauraya.
Mai ciwon suga Kar ya sha, haka wanda madara ke burkucewa ciki Kar ya sha.
AMFANIN SA
1. Yana qarawa namiji yawan ruwan maniyi.
2. Yana qara Qarfin kwakwalwa da gyara tunani.
3. Yana qara sha’awa tsakanin ma’aurata.
4. Yana qarawa Mata Niima.
5. Yana qara yawan jini.
6. Yana qara qarfi da Kuzari a jikin dan adam.
7.Yana qara ruwan nono ga mata.
8. Yana taimakawa namiji Mai Qarancin sha’awa.
A jarraba domin neman dacewa.
Allah ya taimaka.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Karanta wannan bayanin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.