Advertisement
Trending

Matsalolin jima’i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza

Matsalolin jima'i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza

1. RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci “Chlamydia” (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin ƙarfin mazakuta idan ciwon yayi ƙamari ba’a magance shi ba. Cutar maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin ƙarfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken ƙarfin al’aurar namiji ko raguwar ƙarfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miƙewar al’aura yayinda ake buƙatar fara jima’i. Bugu da ƙari, matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin ƙarfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jinɗaɗin rayuwarsa ta jima’i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar bazai iya yima iyalinsa ciki ba saboda rashin miƙewar al’aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala, inshaaAllah.

2 RASHIN HAIFUWA:. Cutar sanyi mai suna “Gonorrhea” (Gonoriya) , kamar dai ƙwayar cutar “Chlamydia”, cutace daga halittar “bacteria” kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, daga nan sai ya koma ɗorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda ɗan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, ƙaikayin dubura, zubar jini, murar maƙoshi/maƙogwaro, jan- ido ko ƙananan kuraje, ciwon gaɓoɓi da sauransu. Idan ba’a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga namiji ko mace.

Nau’in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma kowanne iri akwai ƙwayar halittar dake haddasa ciwon da alamominsa da kuma matakan cutar a jikin ‘dan adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/ƙanjamau (AIDS/HIV) tana daga cikin manyansu saboda itama anfi yaɗata ta jima’i, kuma sau dayawa itace ke gayyatar sauran cututtuka a jikin ‘dan adam.

3) KANKANCEWAR ZAKARI, duk da dai cewa babu wani sahihin bayani a kimiyyance dake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma ƙarami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na ƙorafin cewa sanyi ya sace musu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan ƙanƙancewar alƙalummansu.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima’i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), ‘yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima’i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za’a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen ‘yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. ‘Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, ‘buya idan ba’a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

e) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau’in ciwon.

Ciwon sanyi yana da haɗari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu. Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai cimmasa. Akwai ciwuka masu haɗari sosai kamar AIDS/HIV, wanda zasu iya wargaza iyali. Don haka maison zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai yaji tsoron Allah. Wanda kuma Allah Ya jarabta da ciwon bata hanyar zina ba to sai ya nemi magani, haka shima wanda ya tuba ga Allah. Allah Ya bawa Musulmi lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button