Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Ashe Wanna Shine Dalilin Canza Kudin Nigerian Asiri Yatonu Yanzu

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Ashe Wanna Shine Dalilin Canza Kudin Nigerian Asiri Yatonu Yanzu 👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
NA SALLAMA
Daga Datti assalafy
Wani babban mutum wanda yana cikin Gwamnatin Shugaba Buhari ya fahimtar dani wani sirrin da tunani bai taba hangowa ba akan batun canza fasalin kudin Nigeria a wannan lokaci da ake tunkarar babban zabe na Kasa
Insha Allahu ba zan sake kalubalantar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari Maigaskiya akan haka ba
Tabbas akwai wasu abubuwa na sirri wanda Gwamnati bata fitowa tayi cikakken jawabi a kai, koda ‘yan kasa zasuyi ta korafi da zagi Gwamnati ba zata kula ba, saboda ta san bamu san manufar ba
Zamu fuskanci takuri da wahala na dan lokaci a dalilin canza fasalin kudin, amma karshe abin zai zama alheri garemu Insha Allah
Masu karin magana sukace da tsohuwar zuma ake magani
Allah Ka kara wa Shugaba Buhari lafiya imani, Ka sa Ya wanye da mulkinsa lafiya
Ra’ayi
Chanja fasalin kudi, ko saka Kasa Rudani!
Bahaushe yace mai hali baya barin halinsa, lallai wannan kintacen magana bashida gyara domin kuwa dayawa daga cikinmu yan’adam mukan darsu da wasu aqidu imma masu kyau,ko akasin hakan
Kamar yanda muka kyautata zato akan tsohon Soja, wajen fitowa da kudaden mu, gumi,ruwa, watakil harma da sanyi a wasu sassan kasa don ganin ya lashe zabe, da zummar ganin cewa kakarmu da yanke saka. Kowa dake Kasar tun bayan zabe ya zura idanu yaji wane irin tuki wannan dattijo zaiyiwa milyoyin masoya dasuka sadaukar da komai dominsa. Kwatsam sai aka fara da rufe boda don kasa ta ciyar dakanta, wannan tsari ya matukar kassara mutane, domin illar sa yafi alfanunsa yawa, kowa yasan tunda farashin kayan masarufi yafara hawa to haryanzu sama yake kuma yi. Wanda daga bisani da kansa yafadi cewa rufe iyakokin bai haifar da da’ mai ido ba. Amma hakan bai hanamu toshe kunnuwa dasake bashi dama ta biyu ba saboda aikin Mambila da jawo Ruwan Teku a Baro jihar Neja. Wanda duk wannan yazama lissafin gizo, ba Ruwan ba Wutar.
Muna cikin wannan halin, da murnar zamu jefar da kwallon mangwaro muhuta da kuda, sai kuma ga maganar chanjin kudi mai cike da sarkakkiya da ruda tunani. Alokacin da Manjo yayi chanjin kudi na farko a 1984 zamanin yana Soja kowa yasan yanda Tarihi yayi Alawadai da kassara mutane da yayi, shin kowane barawo kamar yanda yazata.
Idan kabi kasashe dake amfani da cashless, kasashe ne (Developed) wato wanda sukaci gaba mukuma yanzu muke tasowa. Kasar Finland na amfani da wannan tsari amma yawanta mutum million 5.541, Sweden nada 10.42, sai Uwa Burtaniya 55.98 dadai sauran irinsu Germany masu mutum million 83.2 duk a kididdigar 2021.
Haba Shugaba katuna Nigeria nada sama da mutum million dari biyu da wani abu a 2006 census, akwai kauyuka da babu layin waya ballantana bankuna, babu karfin network kamar wadancan kasashe, ga damfara ta yanar gizo. Allah ne kadai yasan iya mutunen da zasu tafka hasara musamman mutanen karkara da sukayi ruwa da zaki SAI BABA lallai yakamata aduba idan domin Talaka akeyi.
Idan kayi duba sanda aka kirkiri kudin kansu mutanen mu basusan boko ba, shiyasa akayi rubutun “ajami” don saukaka musu fahimta. Amma shugaba kayenke hukuncin da kasan mutanen ka zaifi shafa domin sune sukafi tu’ammali da kudade wajen kananan sanao’i ko leburanci. Me yahada makiyayi ko lebura da account, bare mai shoe shiner, ko yakan farce. Allah wadan naka ya lalace.