SIRRIN GYADA GUDA 9 Mafi yawa daga cikin mutane ba su da masaniya kan amfanin da gyada ke yi a jikin mutum.

SIRRIN GYADA GUDA 9 Mafi yawa daga cikin mutane ba su da
masaniya kan amfanin da gyada ke yi a
jikin mutum.
Wasu mutane sun canfi cewa cin gyada
danya,dafaffe ko kuma soyayya na kara
kiba a jiki sannan yana kawo wasu
kuraraji a fuska wanda ake kira da
‘Pinples’.
Ga amfani 9 da gyada ke yi a jikin mutum;
1. Gyada na kare mutum daga kamuwa da
cutar bugawan zuciya.
2. Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin
B3’ wanda ke taimakawa wajen hana
mutum mantuwa.
3. Yana dauke da sinadarin ‘Phylosterols
wanda ke kare mutum daga kamuwa da
cutar daji.
4. Yana kuma kare mutum daga kamuwa
da cutar siga.
5. Ana samun sinadarin ‘Folate’ wanda ke
bunkasa kiwon lafiyan mata masu ciki.
6. Gyada na kara karfi a jiki.
7. Yana bunkasa girman jikin mutum
musamman yara domin yana dauke da
sinadarin ‘Protein’.
8. Gyada na gyara fatar jikin mutum da
hana saurin tsufa saboda akawai sinadarin‘vitamin E’ a ciki.
9. Gyada na faranta wa mutum rai
musamman masu yawan fushi.