Chanjin Kuɗi: Wasu Ma’aikatan Bankin Zenith Sun Tsere Ta Bayan Katanga Saboda Mutane Na Shirin Shigowa

Kamar Yadda Kuka Sani Da Acikin Satukan Nan Ake Ta Samun Matsaloli Na Karancin Kudin Takarda musamman A Nigeria, Kasancewar Sanarwar Da Babban Bankin Kasar Ya Fitar Tare Da Umarnin Shugaban Kasar Muhammad Buhari Akan Chanja Fasalim Kudi Da Kuma Daina Karbar Tsofaffin.
Sai Dai hakan Ya Tayar Zaune Tsaye Kasancewar Mutane Dayawa Suna Shan Wahala Sanadiyyar Wannan Doka Da Aka Fitar Ta Chanja Kudi, Wanda Yasanya Dayawa Daga Cikin Mutane Bazama Bankuna Domin Neman Sababbin Kudin Da Babban Baankin Kasar Ya Fitar Domin Ayi Amfani Dashi Maimakon Tsohon.
Wani Bidiyo Da Mukaci Karo Dashi Yana Yawo Wanda Hotuna Muka Samu Bamu Samu Cikakken Bidiyon Ba, Munga Wasu Daga Cikin Ma’aikatan Bankin Zenith Na Tserewa Ta Katanga Saboda Gudun Kada Al’umma Su Fasa Kofar Bankin Su Shigo Su Far Musu.
A Cigaba Da Rohoton Dalilan jam’iyyu na hana CBN kara wa’adin sauyin kuɗi a Najeriya
Shugabannin jam’iyyun da suka kai babban bankin Najeriya kara kan ka da ya kara wa’adin sauyin kudi daga ranar 10 ga watan Fabrairu, sun ce sun yi hakan ne domin ganin an gudanar da sahihin zaɓe a 2023.
A jiya Litinin ne dai wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta hana Babban Bankin Najeriya da Shugaban ƙasar da wasu bankunan kasuwanci sake ɗagawa ko yin katsalandan da wa’adin 10 ga wannan wata na dakatar da karɓar tsoffin takardun kuɗi.
Rahotanni sun ambato, Mai shari’ah Eneojo Eneche na ba da umarnin na wucin gadi, bayan wasu jam’iyyun siyasa biyar da suka shigar da ƙara gabanta sun nemi hakan .
Jam’iyyun dai sun hada da Action Alliance (AA) da Action Peoples Party, (APP) da Allied Peoples Movement, (APM) da kuma National Rescue Movement (NRM).
‘Sakin mara’
Alhaji Yusuf Ɗan Talle shi ne shugaban jam’iyyar APM mai alamar rogo, kuma Sakataren ƙasa na Majalisar tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa “yanzu zabe saura mako uku kuma mene ne dalilin da ya sa wasu ‘yan siyasa suka damu sai an sake dagewa?
Ka ga kenan akwai tunanin wasu na son a sakar musu mara su samu kudin sayen kuri’a.”
Shugaban na jam’iyyar APM ya kara da cewa “burinmu shi ne a yi sahihin zabe ba tare da an yi amfani da kudi ba.
Domin hakan zai bai wa kananan jam’iyyu irin namu wajen cin zabe tunda mu ba mu da kudin sayen kuri’a.”
Barazanar kaurace wa zaɓen 2023
Da ma dai Jam’iyyun siyasa 13 daga cikin jam’iyyu 18 a Najeriya sun yi barazanar kaurace wa babban zaɓen ƙasar da ke tafe matukar Babban Bankin Ƙasar ya ƙara wa’adin amfani da tsoffin kuɗi a ƙasar.
Jam’iyyun sun ce ba za su shiga zaɓen ba matuƙar CBN ya sake tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun kudin.
Gamayyar ƙungiyar shugabannin jam’iyun, waɗanda suka yaba wa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari kan sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, sun dage cewa dole a tabbatar da tsarin.
Shugaban Jam’iyyar Action Alliance A.A Kenneth Udeze, wanda ya yi wa manema labarai jawabi, ya ce ”muna bayyana cewa akalla jam’iyyu 13 daga cikin jam’iyyun ƙasar nan 18 ba za mu shiga zaɓen da ke tafe ba matuƙar aka dakatar ko a aka soke ko aka tsawaita wa’adin fara amfani da sabbin takardun kuɗi”.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara suka kai ƙarar gwamnatin tarayya gaban Kotun Ƙolin ƙasar, suna neman kotun da ta dakatar da gwamnatin tarayyar daga aiwatar da tsarin wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗi da Babban Bankin ƙasar ya ɓullo da shi.
Matakin da gamayar jam’iyyun suka yi watsi da shi.
A makon da ya gabata ma dai gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki suka gana da shugaban ƙasar a fadarsa da ke Villa.
Inda suka buƙace shi da ya sake tsawaita wa’adin amfani da sabbin takardun kudi, sakamakon wahalhalun ƙarancin kudin da jama’ar ƙasar ke fuskanta.
To sai dai a martanin da ya mayar, shugaban ƙasar ya alƙawarta duba tare da magance matsalar cikin kwanaki bakwai.